1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fiye da mutane 140 sun mutu a hare haren da aka kai jiragen kasa a Bombay

July 11, 2006
https://p.dw.com/p/Buqo

Akalla mutane 140 suka rasu sannan sama da 200 sun jikata a jerin hare haren bama bamai da aka kai kan jiragen kasa a birnin Bombay wato Mumbai na kasar Indiya.A halin da ake ciki an dauki matakan ko-takwana a dukkan manyan birnen kasar bayan wadannan munanan hare haren da aka kai a wannan birni mai mutane miliyan 14 kuma cibiyar kasuwanci a Indiya. Rahotanni sun nunar da cewa abubuwa guda 7 suka fashe a cikin jiragen da kuma dandamali hawa jirgi a lokacin da mutane ke hada-hadar komawa gida bayan sun tashi aiki da maraice. Shugaban hukumar dake kula tsaro na zirga zirgar jiragen kasa na Western Railways a Bombay Anail Sharma ya ce yanzu haka a rufe dukkan tashoshin jiragen kasa a birnin sannan sai ya kara da cewa: “An kai hare haren ne a tsawon mintoci 10 tsakani. Ko-ina ya bi ya rude. Ko shakka babu wannan wani shiri ne da aka tsara shi a tsanake.”

FM Indiya Manmnohan Singh ya ce ko shakka babu hare haren aikin ´yan ta´adda ne. Shi ma shugaban Pakistan Pervez Musharraf ya yi Allah wadai da hare haren.