1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fiye da mutane 50 sun mutu a fashewar wasu bama-bamai 3 a birnin New Delhi

October 29, 2005
https://p.dw.com/p/BvNO

Akalla mutane 50 sun rasu sannan das dama sun samu rauni a wasu jerin hare haren bam da aka kai a New Delhi babban birnin Indiya. Da yawa daga cikin wadanda fashewar bama-baman ta rutsa da su dai mata ne da kananan yara. Kamar yadda hukumomi suka nunar bama-bamai 3 suka fashe mintoci kalilan bayan juna a cikin wasu kasuwanni dake cike da jama´a sai kuma daya da ya fashe a cikin wata safa. Daya daga cikin kasuwar ta na a wata unguwa ne da baki ´yan yawon shakatawa ke yawaita zuwa. Kakakin FM Indiya Manhoman Singh ya bayyana fashewar bama-baman da cewa wani aiki ne na ta´addanci. Kawo yanzu ba wanda yayi ikirarin hannu a hare-haren wadanda suka zo kwanaki 3 gabanin bikin ´yan Hindu da ake kira Diwali da za´a yi a ranar talata.