1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fradique de Menezes ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a Sao Tome da Principe

August 8, 2006
https://p.dw.com/p/BunN

A cen kuwa tsibirin Sao Tome da Principe, tunni hukumar ta bayana sakamakon ƙarshe na zaɓen shugaban ƙasa,da a ka shirya ranar 30 ga watan juli da ya gabata.

Shugaba Fradique de Menezes, yayi tazarce tun zagaye na farko, tare da samun kussan kashi 60 bisa 100, na jimmilar ƙuri´unda aka kaɗa.

Ɗan takara na 2, wato Patrice Trovada, ya tashi da kussan kashi 40 na wannan ƙuri´un.

Sai kuma na 3, da ya zo ƙutal, wato Nilo Guimares da ya samu ƙasa da kashi ɗaya,bisa 100 na yawan ƙuri´un.

Sakamakon ya nuznar da cewa, kussan kashi 65 bisa 100, na al´umomin ƙasar, su ka gudabar da zaɓe.

A sahiyar yau, hukumar zaɓe ta gabatar da sakamakon ga kotun ƙoli ta ƙasar.

Yan kallo daga ƙetare, sun tabbatar da cewa, wannan zabe,ya wakana lami lahia, ba tare da shirya maguɗi ba.

Ranar 3 ga watan satumber mai zuwa, a ka shirya rantsar da shugaba De Menezes.