1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

France da Britania sun bayyana sanarwar haɗin gwiwa a game da rikicin Darfur

July 27, 2007
https://p.dw.com/p/BuFM

A wata sanarwar haɗin gwiwa, ministocin harakokin wajen France da na Engla, sun yi kira ga gwamnatin Sudan da yan tawaye su mutunta yarjeniyoyin zaman lahiar da a ka cimma tsakaninsu.

Ƙasashen 2 sun cimma daidaito, a game da batun haɗa ƙarfi da husa´o´i, domin magance rikicin yankin Darfur.

Sanarwar ta Bernard Kouchner da David Miliband, ta ƙasashe France da Britania, na aiki kafaɗa da kafaɗa a Majalisar Ɗinkin Dunia da zumar aika rundunar shiga tsakani cikin gaggawa.

A ɗaya ɓangaren,

komitin mussamman na Majalisar Ɗinkin Dunia, mai kulla da kare haƙƙoƙin bani adama , ya yi suka da kakkausar halshe ga hukumomin Sudan, a game da tallafin da su ke baiwa mayaƙan Janjawid a yankin Darfur.

Komitin yayi Allah wadai ga wannan ɗabi´a ta gwamnati, wadda ya dangata da ƙabilanci.

Rahoton da komitin ya gabatar a yau juma´a, ya buƙaci hukumomin Khartum su daina bada talafi ga yan Jandjawid, sannan su gudanar da bincike, domin hukunta dukkan wanda a ka samu da hannu, a rurar wutar rikicin yankin Darfur.