1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Francois Bozize zai tsaya takara

Gazali Abdou TasawaAugust 8, 2015

Jam'iyyar tsohon shugaba Bozizé ta KNK ce ta tsayar da shi takara bayan babban taronta a Bangui kuma zai fafata da sauran 'yan takaran mukamin su 100.

https://p.dw.com/p/1GC8n
Präsident der Zentralafrikanischen Republik - Francois Bozize
Hoto: Getty Images

A kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, jam'iyyar adawa ta Kwa Na kwa ta kaddamar da tsohon shugaban kasar Francois Bozize a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasa da kasar za ta gudanar a watan Oktoba mai zuwa. Wannan mataki ya biyo bayan wani taron congress da jam'iyyar ta KNK ta shirya a ran Juma'a a birnin Bangui.

Taron jam'iyyar ta KNK ya wakana ne ba tare da Francois Bozizen tsohon shugaban kasar ta Jamhuriya Afirka ta Tsakiyar, wanda sojoji suka kifar da mulkinsa a cikin watan Maris din shekara ta 2013 ya halarta ba, kasancewa yana zaman gudun hijra inda ya ke safa da marwa tsakanin kasashen Kenya da Uganda tun daga wancan lokaci.

Kimanin 'yan takara dari ne ke tsayawa takarara neman mukamin shugaban kasa a zaben na watan Oktoba mai zuwa.