1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

G20: Amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen warware rikici

Abdullahi Tanko Bala
February 17, 2017

Taron na G20 da aka kammala a wannan Jumma'a a birnin Bonn ya ja hankalin Shugaban Amirka Donald Trump da ya guji abin da zai jawo mayar da Amirkar saniyar ware.

https://p.dw.com/p/2XmxM
Deutschland G 20 Außenministertreffen in Bonn
Taron ministocin harkokin waje na G20 a birnin Bonn na JamusHoto: DW/A. Freund

Tun gabanin taron dai an yi ta baiyana ra'ayoyi mabambanta akan alkiblar da muhawarar taron za ta dosa a daidai lokacin da ake cikin rashin tabbas game da sakon farko na Amirka ga taron wanda zai shata manufofin dangantakarta da sauran kasashen duniya. Sai dai kuma kamar yadda akan ce fata na gari lamiri, kasashe kawayen Amirka sun sami albishir mai karfafa gwiwa daga sabon sakataren harkokin wajen Amirkar Rex Tillerson wanda ya ce Washington ta bada cikakken goyon baya ga shawarar da aka cimma bisa jagorancin Majalisar Dinkin Duniya na daukar matakan diplomasiyya domin samun masalaha ga rikicin Siriya. wannan dai wata alama ce da ke nuna cewa Trump zai ci gaba akan manufofin da ake kai a yanzu.

Tillerson ya samu damar ganawa da takwarorinsa

Deutschland Bonn G20
Rex Tillerson na Amirka, da Sigmar Gabriel na JamusHoto: picture-alliance/ZUMAPRESS.com/G. Johnson

Tillerson ya yi amfani da taron na G20 a nan Jamus domin yin wasu tarukan bayan fage da takwarorinsa na sauran kasashen duniya domin nazarin matsaloli, kama daga rikicin Koriya ta Arewa zuwa Ukraine. A irin wadannan taruka, babban jami'in diplomasiyyar na Amirka ya bi sahun rukunin wasu kasashe domin tattauna yadda za a kawo karshen yakin da aka shafe shekaru shidda ana yi a Siriya.

Bai wa hanyoyin diflomasiyya karfi wajen warware rikici

Dukkan mahalarta taron dai na bukatar daukar matakai ne na diplomasiyya saboda matakin karfin soji kadai ba zai taba kawo zaman lafiya a Siriya ba. Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel ya ce duniya na bukatar hadin kai ne ba rarrabuwa wajen sulhunta rikici rikice-rikice ba.

Deutschland G 20 Außenministertreffen in Bonn PK Gabriel
Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar GabrielHoto: Reuters/T. Schmuelgen

" Yace babu shakka kowa ya san cewa muna bukatar hadin kan gamayyar kasa da kasa domin shawo kan matsaloli da suka yiwa duniya dabaibayi, kuma sakataren harkokin wajen Amirka shi ma ya fayyace wannan. sannan a tattaunawar da muka yi a yau, muna fatan ci gaba da su a dukkan matakai. Ina kuma ganin cewa Rex Tillerson zai kasance abokin hulda wanda za mu aiwatar da dukkan matakin da ake bukatar dauka na bai daya da kuma karfafa dangantaka tsakanin kasashe."

A na shi bangaren ministan harkokin wajen Faransa Jean-Marc Ayrault ya shaida wa yan jarida cewa akwai matukar muhimmanci a yi tattaunawa da kut da kut da Amirka kan Siriya da kuma wasu bututuwa. Kasashen da aka tattauna da su kan batun Siriyar bayan Jamus da Faransa sun hada da Britaniya da Jordan da hadaddiyar daular Larabawa, da Qatar da Turkiyya da kungiyar Tarayyar Turai da kuma Saudiyya. A karshen taron na yini biyu, ministocin gamayyar kasashen na G20 sun amince cewa samun nasarar warware rikicin Siriya da Ukraine ba zai samu ba, ba tare da an shigar da Rasha ba.