1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

GABATAD DA CIBIYAR HORAD DA JAMI'AN CETO TA AHWEILER

Yahaya AhmedDecember 22, 2003
https://p.dw.com/p/Bvmz

Wannan cibiyar, an kafa ta ne don tsara shirye-shiryen matakan gaggawan da za a dauka, idan hadari ko kuma wata annoba ta auku da nufin ba da taimako ga wadanda abin ya shafa ba tare da wani bata lokaci ba, da kuma kare sauran jama'a da kadarori. A ko yaushe dai, akwai wani rukuni da ake bai wa horo a cibiyar, ko na soji , ko na `yan kashe gobara, ko kuma ma'aikatan kungiyoyin ceto da ba da taimakon agaji.

Da ma can, jami'an da ke samun horon na cikin shiri ne na ko ta kwana. Da dai an ba da sanarwar wata annoba ta lasifika, nan take sai ka jami'an sun shiga kai-kawo, don shirya kayan aikinsu su je gun da matsalar ta wakana. A was lokutan kuma, ana iya yin gwaji kawai don gano irin hali na shirin da jami'an ke ciki:-

"Ana ci gaba da gina garu don tare ambaliyar ruwa. Jirgin kasa na cikin gari mai lamba 6 ya daina aiki. Ruwa ya kusa cinye tsibirin Steinhaus. Tuni dai an kwashe kusan mutane dari 2."

Wannan sanarwar dai, misali ne na irin gwajin da masu horaswa a cibiyar ke yi. A nan dai, wani dan karamin gari ne ke huskantar ambaliyar ruwa. Sabili da haka, duk kafofin ceto kamar na `yan kwana-kwana da Red Cross da dai sauransu, na jan damara idan matsaloli irin wannan suka auku. Shugabanin rukunan da za a tura gun annobar, suna nan suna ta shawarwari kan matakan gaggawar da za a iya dauka nan take. A jikin bango dai, ga alamu daban-daban, wadanda ke nuna inda ko wani rukuni zai kasance. Kazalika kuma, akwai taswirar da ke nuna hanyoyi mafi saukin da za a iya bi zuwa gun, da kuma wadanda za a iya toshewa don hana cinkoson motoci. An kuma alamta gine-ginen da za a iya kai masu rauni cikin gaggawa don ba su taimako, kafin ma a kai su asibitoci mafi kusa da gun hadarin. Ta hakan ne dai za a iya cim ma nasarar bayyana wa ko wane rukuni irin aikin da zai yi da kuma inda zai fara aikin. Rainer Blumenrath, wani ma'aikaci na kungiyar kwana-kwana, wanda ya ziyarci irin wadannan kwasakwasan a cibiyar. Ya bayyana cewa:- "Babbar fa'idar da ake samu idan an halarci irin wannan kwas din, ita ce muna iya saduwa da takwarorinmu na wasu jihohin tarayya, inda muke kara wa juna ilimi da kuma yin musayar ra'ayoyi. Hakan kuwa na da muhimmanci kwarai, saboda muna iya karuwa da yadda aka shawo kan wasu matsalolin a wasu wurare."

Cibiyar, da ke Ahweiler kusa da birnin Bonn, tsohuwar fadar gwamnatin tarayya, ita kadai ce irinta a duk fadin tarayya. Sabili da haka ne kuwa, a ko yaushe ake samun maziyarta wani taron bita daga wata jiha ta tarayya. A kowace shekara, ana gabatad da kwasa-kwasai kusan dari 4 a wannan kafar.

Ana dai yin tanadi ne na horad da jami'an wajen iya daukan matakai cikin gaggawa, ko yaushe wata annoba ta auku. Akwai dai rukunai da ke karkashin gwamnatin tarayya, wadanda aikinsu ne kare jama'a lokacin yaki. Wasu rukunan kuma, wadanda su karkashin hukumomin jihohi suke, aikinsu ne ba da taimakon agajji cikin gaggawa a lokacin wata annoba ko kuma wani mugun hadari. Amma idan matsalar ta yi tsamari, duk rukunan na iya mara wa juna baya. A wasu lokutan kuma, ana iya bukatar taimakon agaji daga Jamus, idan wata annoba ta auku a wata kasar ketare. To ta yaya jami'an da za a tura can za su iya gudanad da aikinsu k Frank Jörres, wani ma'aikacin kungiyar Red Cross ta nan Jamus, wanda kuma ke horaswa a cibiyar ta Ahweiler, ya bayyana cewa loto-loto ya kan shirya taron bita ga ma'aikatan ceto da jami'an ba da taimakon agaji, inda ake bayyana musu yadda za su iya aiki a ketare, a duk inda ake bukatar taimako, da kuma yadda za su iya gudanar da aikinsu tsakanin fararen hula da sojoji:- "Muna ba su horo ne kan yadda alal misali, Majalisar dinkin Duniya da sauran kafofinta na musamman, ke gudanad da ayyukansu a wurare daban-daban na duniya. Ana kuma bayyana musu yadda kungiyoyin ba da taimamkon agaji kamar dai kungiyar kasa da kasa ta Red Cross ke gudanad da aikinta. Kazalika kuma, ana fadakad da su game da yadda manyan hukumomi kamarsu kungiyar Hadin Kan Turai ke hidimar samad da kudaden da za a kashe wajen ba irin wannan taimakon a ketare." A ganin Dietrich Läpke, shugaban cibiyar ta Ahweiler, nan gaba aikin da wannan kafar ke yi zai bunkasa ne ya zamo na kasa da kasa. Saboda misalai da yawa na nuna cewa, annoba kamar ambaliyar ruwa, ba a iyakar wata kasa kawai take tsayawa ba. Sabili da haka ne kuwa, yake ganin sai an sami hadin kai tsakanin cibiyoyi irin tasa, kafin a iya shawo kan manyan bala'o'in da ke aukuwa a yankuna daban-daban na duniya. Cibiyar ta Ahweiler dai, inji Läpke, a shirye take ta ba da tata gudummuwa don cim ma wannan gurin.