1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gadhafi ya tauye hakkin bil Adam a Libya

June 23, 2010

Amnesty International ta zargi Libya da zama ɗaya daga cikin ƙasashe da suka fi tauye hakkin bil Adama a duniya.

https://p.dw.com/p/O0Ye
Shugaba Gadhafi na LibyaHoto: AP

Ƙungiyar Amnesty Internatinal ta zargi Libya da ci gaba da musguna wa jama'a duk da cire mata takunkumin karya tattalin arziki da ƙasashen duniya suka yi. Cikin wani rahoto da ƙungiyar ta kasa da kasa ta wallafa a wannan laraba a cibiyarta da ke birnin London, ta ce ba wani ci gaba mai ma'ana da aka samu a kasar ta Lybia a waɗannan shekaru huɗu na baya-bayannan a fiskar kare hakkin bil Adama.

Amnesty ta ce aiwatar da hukuncin kisa, da kuma tauye hakkin fadan albarkacin baki na neman zama ruwan dare a Lybia. ƙungiyar ta ce da akwai bukatar kasar da Mohammad khaddafi ke shugabanta, ta yi ma dokokinta da suka shafi hakkin mutane gyaran fiska domin samun daidaito da sauran kasashen duniya a wannan siga. Hakazalika Amnesty ta nemi Lybian da ta soke hukunci kisa da kuma na bulala da kasar ke amfani da shi wajen hukunta wasu manyan laifuka.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru aliyu