1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gagarumin hadari ya hana taron kolin ASEAN

December 8, 2006
https://p.dw.com/p/BuYl

Wani gagarumin hadari daya taso a safiyar yau juma´a a kasar Phillipines, ya haifar kungiyyar kasashen gabashi da kudancin Asia dage taron kolin ta.

Taron , wanda aka shirya yi a yau, a garin Cebu dake da nisan kilomita 600 daga birnin Manila, an dage shine izuwa watan Janairun sabuwar shekara.

To amma a waje daya wasu rahotannin sun nunar da cewa daukar matakin na da nasaba ne da gargadi da kasashen yamma suka yi, na cewa akwai barazanar kai musu harin kunar bakin wake.

Kungiyoyi na yankin da suka shirya gudanar da zanga zangar bore sun bayyana dalilin dage taron da cewa, hujjoji ne da basu da tushe balle makama.