1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta'addancin 'ya'yan kungiyar Boko Haram

Mösch Thomas /Abdul-raheem Hassan/ LMJAugust 5, 2015

Yunkurin kungiyoyi masu zaman kansu da kuma dai-daikun mutane wajen tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa da su a Najeriya

https://p.dw.com/p/1GALi
Nigeria Flüchtlinge wegen der Offensive gegen Boko Haram
Hoto: Reuters/A. Sotunde

A Najeriya yanzu haka wasu dai-daikun mutane sun fara kafa kungiyoyi domin tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa. Saratu Abiola daya ce daga cikin mutanen da suka yi irin wannan kokari. Ta bude wani shafi mai sunan Testimonial Archive Project domin tallafawa mutanen da rikicin Boko Haram ya tagayyara. A hirar da ta yi da tashar DW Saratu Abiola ta bayyana cewa abune mai wuya a kasa kamar Najeriya kulawa da marasa galihu musamman wadanda suke karkara tana mai cewa:

"A gaskiya akwai cin fuska, saboda siyasa ko dadin mulki ba sa mayar da hankali a kan halin kunci da al'umma ke ciki ganin matsalar ba ta shafesu ba. Akwai bukatar a sani cewa suma 'yan uwanmu da ke fuskantar barazana a Arewa maso Gabas 'yan Najeriya ne, a saboda haka dole a mayar da hankali a kan abin da ke faruwa a kasar nan. Ko da baka yankin akwai bukatar a matsawa gwamnati lamba wajen ganin ta tabuka abin da ya dace."

Halin da 'yan gudun hijira ke ciki a Najeriya
Halin da 'yan gudun hijira ke ciki a NajeriyaHoto: Katrin Gänsler

Hada kai da kungiyoyin fararen hula

Saratu Abiola dai ta hada kai ne da kungiyoyin fararen hula da ke yankuna masu fama da hare- haren Boko Haram, wanda hakan ne ya bata damar ganawa da mutanen da rikicin ya dai-daita kamar yadda ta yi karin haske.

Ta ce: "Mun yi aiki da kwararru musamman wadanda ke da masaniya a kan asarar da rikicin ya haddasa, mun kuma samu wadanda suka rabu da muhallinsu da matan da akai wa fyade da ma batutuwan da suka shafi cin zarafin dan Adam, mun gana da mutanen da abin ya shafa kai tsaye, to amma ba mu samu damar yin magana da sojojin Najeriya ba sai dai mun tattauna da 'yan kato da gora a kan yadda suke gudanar da ayyukansu."

Amfani da kafar adarwa ta Internet

Da yake kawo yanzu al'umma da dama na ziyartar shafin da Saratu Abiola ta bude da zummar sanin halin da al'umma ke ciki da ma makasudin fara wannan gagarumin aikin da ta sa a gaba, ko ya ta ke ji a kan tasirin da shafin nata ke da shi ga yankunan da suke fama da rikece-rikcen? Ga abin da take cewa:

Nasarar ceto wasu mutane daga Boko Haram
Nasarar ceto wasu mutane daga Boko HaramHoto: picture-alliance/AP Photo/J. Ola

"Baya ga damar da kafafen yada labarai da kungiyoyi masu zaman kansu ke samu na sani da kuma baiyana halin da al'ummar ke ciki, ina kuma samun damar musayar bayanai da masu bincike da kan yi nazarin tsare-tsaren da ya dace sannan hukumar tsaron Najeriya na amfani da shafin wajen yada bayanai ga yankin, ina dai ganin akwai ci gaba matuka."

A yanzu dai Saratu Abiola na amfani ne da aljihunta wajen gudanar da wadannan aiyuka, ta kuma bukaci kungiyoyi masu zaman kansu da kuma gwamnati da su yi la'akari da halin da 'yan gudun hijira sama da miliyan guda ke ciki a Najeriya da ma wadanda suka tsallaka zuwa kasashe makwabta irin su Nijar da Kamaru da Chadi.