1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gamayyar ƙungiyoyin sa kai na Jamus na neman ƙarin taimako ga ƙasar Lebanon

Yahaya AhmedAugust 23, 2006

Ƙungiyoyin sa kai na Jamus, sun yi kira ga jama'a da su ƙara ba da taimako don tallafa wa al'umman ƙasar Lebanon, waɗanda a halin yanzu ke fama da wahalhalu iri-iri, sakamakon yaƙan ƙungiyar Hizbullahi da Isra'ila ta yi a ƙasar har tsawon makwanni 4.

https://p.dw.com/p/BtyZ
Sojojin Isra'ila na harba rokoki zuwa kudancin Lebanon a yaƙin da suka yi da ƙungiyar Hizbullahi.
Sojojin Isra'ila na harba rokoki zuwa kudancin Lebanon a yaƙin da suka yi da ƙungiyar Hizbullahi.Hoto: AP

A kudancin ƙasar Lebanon ne aka fi neman taimakon agaji cikin gaggawa, don kulawa da lafiyar ɗimbin yawan jama’ar da yaƙin da Isra’ila ta yi Hizbullahi ya addabe su. Ɗimbin yawan jama’a ne ke huskantar rashin ruwan sha mai tsabta, sa’annan kuma hare-haren da jiragen Isra’ila suka kai a yankin, sun ragargaza gadoji da manyan tituna, abin da ke janyo wa ƙungiyoyin ba da taimakon agaji wasu matsalolin kuma na kai ga al’umman yankunan karkara. Har ila yau dai, an ƙiyasci cewa, za a shafe fiye da shekara ɗaya, kafin a iya tono duk nakiyar ƙarƙashin ƙasar da aka bibbine a yankin kudancin Lebenon ɗin.

Gamayyar ƙungiyoyin sa kan Jamus sun yi gargaɗin cewa, ka da a mai da hankali kawai kan fafutukar ba da gudummowar soji ga rundunar kare zaman lafiyar da ake shirin turawa zuwa kudancin Lebanon ɗin. Shugaban gamayyar, Manuela Rossbach, ta bayyana nadamar ƙungiyoyin ga yadda gwamnatin Jamus ke tinkarar wannan lamarin, wato ta fin mai da hankalinta kan yawan dakarun da Jamus za ta iya bayarwa ga rundunar kare zaman lafiyar:-

„Damuwarmu, ita ce taƙaita rikicin Gabas Ta Tsakiyan kan yawan dakarun da gwamnati za ta iya turawa kawai, ba tare da yin la’akari da matsalolin da jama’a suka yi ta huskanta ba, sakamakon yaƙin da aka yi ta gwabzawa har tsawon makwanni 4. A ƙalla dai, a Lebanon ɗin kawai, kusan mutane rabin miliyan ne suka kaurace wa matsugunansu suka zamo ’yan gudun hijiran dole a arewacin ƙasar ko kuma a Siriya. Tun tsagaita buɗe wutar dai kusan mutane dubu ɗari 4 ne suka dawo. Gaba ɗaya kuma, mutane dubu ɗari 6 ne a halin yanzu suka kasance ba su da matsugunai kuma.“

A Lebanon ɗin kawai, fiye da mutane dubu da ɗari 2 ne suka rasa rayukansu, sakamakon farmakin Isra’ilan, kuma fiye da dubu 4 ne suka ji rauni. Gamayyar ƙungiyoyin sa kan ta Jamus dai ta yi marhabin da tsagaita buɗe wutar da aka cim ma, kuma tana fatar cewa za a cim ma daidaito wajen girke dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a yankin ƙarƙashin ƙuduri mai lamba 1701 da aka zartar a kwamitin sulhu na Majalisar. A kan wannan batun dai, Roßbach ta bayyana cewa:-

„Muna kira ga gamayyar ƙasa da ƙasa da ta cika alkawarin da ta ɗauka lokacin da ake tsara ƙuduri mai lamba 1701, musamman a lokacin da za a yi taron neman taimako ga kasar Lebanon ɗin. Samad da wani tsari na tabbatad da zaman lafiya mai ɗorewa ne kawai abin da zai iya warware rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya.“

A taron ƙasashe masu ba da tallafi da za a yi a birnin Stockholm a ran 31 ga wannan watan, Rossbach ta kyautata zaton cewa, za a iya tara kusan Euro miliyan ɗari da 90 don tallafa wa ƙasar Lebanon. Ana dai bukatar wannan kuɗin ne don samar wa mutanen da matsalar ta fi addaba magunguna, da ruwan sha mai tsabta da abinci da kuma matsugunai. Gamayyar ƙungiyoyin sa kan ta Jamus ta ce har ila yau dai ba ta sami taimako isasshe kamar yadda ta zata ba.

Wani jami’in gamayyar, Thomas Schwarz, wanda ya dawo ba da daɗewa ba daga Lebanon, ya yi kira ga jama’ar Jamus da su nuna zumunci ga mutanen Lebanon, su ƙara ba da taimako don a iya tallafa wa ɗimbin yawan yara ƙanana da wannan yaƙi ya janyo musu bala’i.