1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gamayyar jam'iyyu masu mulkin Potugal sun lashe zabe

Suleiman BabayoOctober 5, 2015

Firaminista Pedro Passos Coelho na Potugal ya sake dawowa kan madafun iko bayan gamayyar jam'iyyu masu mulkin sun sake lashe zabe.

https://p.dw.com/p/1GidB
Parlamentswahlen Portugal - Sieger Pedro Passos Coelho
Hoto: REUTERS/Rafael Marchante

Gamayyar jam'iyyu da ke mulkin kasar Potugal sun samu nasara yayin zaben wannan Lahadi da ta gabata, duk da cewa masu ra'ayin sauyin sun rasa gagarumin rinjayen da suke da shi a majalisar dokokin kasar mai kujeru 230.

Gamayyar masu mulkin sun samu kashi 32 cikin 100 na kuri'un da aka kada, sannan 'yan adawa masu ra'ayin gurguzu suka samu kashi 32 cikin 100.

Sakamakon zaben ya tabbatar da cewa Firaminista Pedro Passos Coelho ya sake dawowa kan madafun iko ke nan, kuma ya ce yanashirye da hada kai da 'yan adawa, domin karfafa tattalin arzikin kasar da rage yawan kudaden da ake bin kasar bashi, inda kasar take ci gaba da aiwatar da matakan tsuke bakin aljihu tun shdekara ta 2011.