1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gambiya: Adama Barrow ya cika watanni shida a kan mulki

Suleiman Babayo
July 19, 2017

Al'ummar kasar Gambiya na mayar da martani kan kamun ludayin gwamnatin shugaba Adama Barrow bayan da ta cika watani shida a kan madafun ikon kasar.

https://p.dw.com/p/2gnQa
Gambia Präsident Adama Barrow | Amtsübernahme & Einweihungszeremonie in Bakau
Shugaban kasar Gambiya Adama Barrow lokacin da aka sake rantsar da shi a birnin Banjul.Hoto: Reuters/T. Gouegnon

Zaben na watan Disamba na shekarar da ta gabata ta 2016 ya bayar da mamaki, inda shugaba Yahya Jammeh da ya shafe kimanin shekaru 22 kan madafun iko ya sha kaye a hannun sabon shiga cikin harkokin siyasa Adama Barrow. Dubban mutane suka bazama kan titunnan birnin Banjul fadar gwamnatin kasar domin nuna jin dadi kan yadda dan kasuwa Adama Barrow ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasa, kuma duk da takaddama d hakan ya kawo karshen gwamnatin kama karya ta Yahya Jammeh. Watanni shida bayan Barrow ya dauki madafun iko akwai 'yan kasar da suke gannin har yanzu gwamnatin babu wanda yasan inda ta dosa kamar yadda Mariama Danso daliba mai nazarin Turancin Ingilishi a jami'a ke cewa:

Gambia Markt in Banjul
'Yan kasar Gambiya na harkokinsu na kasuwanci a kasuwar birnin Banjul.Hoto: Reuters/A. Sotunde

"Ban yi tsammani an samu nasarori a fannin ci-gaba ba. Akalla a nuna wa mutane hanya. A ce ga abin da gwamnati ta saka a gaba ke nan. Amma har yanzu mutane suna watangariri. Akwai rashin sanin inda aka dosa da hargitsi, babu wanda ya san inda muka nunfa. Jammeh ya tafi, mun kawar da shi daga madafun iko, kuma ya tafi. Ina tsammani abin da gwamnati za ta yi shi ne daina daura alhakin duk abin da ke faruwa kansa. Amma ya dace mu samar da mafita daga matsalolin da muke ciki."

Shi dai shugaba Adama Barrow na Gambiya ya samu nasara sakamakon yadda tsohon Shugaba Yahya Jammeh ya garkame shugabannin 'yan adawa da suka zama masa kadangaren bakin tulu. Tun farko ya amince da sakamakon amma daga bisani ya sauya ra'ayi abin da ya janyo kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS-CEDEOA ta yi barazana tare da tura dubban sojojin domin kifar da gwamnatin da karfi, lamarin da ya saka Jammeh ya mika wuya tare da tafiya gudun hijira na siyasa a kasar Equatorial-Guinea. Lamin Saidykhan yana ganin sabuwar gwamnatin ta Gambiya ta samu nasara kan inganta harkokin demokaradiyya:

Senegal Unterstützer des gambischen neugewählten Präsident Adama Barrow in Dakar
Matasa da ke nuna murnarsu lokacin rantsar da Adama Barrow a birnin Dakar na Senegal.Hoto: Reuters/T. Gouegnon

"Ina tsammani an samu nasarori, an daina gallaza wa mutane saboda ra'ayinsu. Ana mutunta tsarin demokaraddiya."

Wannan karamar kasa ta Gambiya da ke yankin yammacin Afirka ta kasance daya daga cikin inda ake samun dubban matasa masu neman kai wa kasashen Turai domin samun rayuwa mai inganci, kuma gwamnatin shugaba Adama Barrow tana aiki game da shawo kan wadannan matsaloli.