1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gambiya ta koma kungiyar Commonwealth

February 15, 2017

Shugaba Adama Barrow na Gambiya ya ce kasarsa za ta koma kungiyar Commonwealth kana da dakile shirin fita daga kotun duniya mai hukunta manyan laifukan yaki.

https://p.dw.com/p/2Xa14
Gambias Präsident Adama Barrow während einer Pressekonferenz in Banjul
Hoto: Reuters/T. Gouegnon

Shugaba Adama Barrow  na kasar Gambiya ya bayyana cewa kasar za ta koma cikin kungiyar kasashe rainon Birtaniya ta Commonwealth, kana an dakile shirin kasar na fita daga kotun duniya mai hukunta manyan laifukan yaki.

Shugaban ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da Sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson. Tsohon Shugaba Yahya Jammeh ya tsame kasar ta Gambiya daga kungiyar Commonwealth a shekara ta 2013, sannan ya fara shirin janye kasar daga kotun duniya mai hukunta manyan laifukan yaki.

Sabon shugaban ya na neman hanyoyin da zai farfado da darajar kasar ta Gambiya tsakanin kasashen duniya, tun bayan lashe zaben watan Disamba a wannan kasa da ke yankin yammacin Afirka.