1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gananawar Blair da Erdogan a Ankara

December 16, 2006
https://p.dw.com/p/BuXg

A rangadin aikin daya kaddamar a yankin gabas ta tsakiya a jiya jammaa,Premiern Britania Tony Blair ya gana da takwararsa na Turkiyya Tayyip Erdowan,adangane da yadda zaa sake farfado da shirin zaman lafiya tsakanin Palasdinawa da Izraela.Shugaban gwamnatin Britanian wanda ke daukan matakan ganin cewa an farfado da shirin zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu kafin saukarsa daga mukami a shekara mai kamawa,na neman hadin kann kasashen musulmi wajen taimakawa jan hankalin izraela da Palasdinu,komawa teburin tattaunawa.Wannan ziyara tasa dai tazo adaidai lokacin da yankin Palasdinawan ke fama da rigingimu na cikin gida,wanda ya jagoranci fadan fito na fito da bindigogi tsakanin bangarorin adawan yankin,wanda kuma ke barazanar jefa yankin cikin yakin basasa.