1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawa tsakanin Abbas da Olmert a Jericho

August 6, 2007
https://p.dw.com/p/BuEa

Nan gaba a yau ne shugaban hukumar Palestinawa Mahmud Abbas, da Praminista Isra´ila Ehud Olmert, za su gana a birnin Jericho dake yamma ga kogin Jordan.

Wannan taro da ka wa takenmai mahimmanci zai duba matsalolin da su ka hana ruwa guidu a yunƙurin kawo ƙarshen rikici tsakanin Isril ada Plaestinu.

Wanda shine karon farko tun shekaru 6 da su ka wuce, da wani magabacin Isra´ila ya taka ƙafa a birnin Jericho.

Wani mai magana da yawun hukumar Palestinawa ya ce batutuwa masu mahimmanci guda 3 ne, za su mamaye ajendar taron wato, ƙayyade iyakokin Isra´ila, matsayin birnin Ƙudus, da kuma matsalar yan gudun hijira Palestinu.

A sakamakon wannan taro ɓangarorin 2, za su girka wani komiti, wanda zai ci gaba da lalubo hanyoyin cimma tudun dafawa.

Bayan ziyara da ta kai makon da ya gabata a gabas ta tsakiya, sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice ta dangata taronna yau a matsayin wani mataki, na

Bayyanawa dunia kyaukyawan burin Olmert da Abbas, na girka ƙasashe 2, wato Isra´ila da Palestinu, wanda za su dangataka ta cuɗe ni in cuɗe ka.