1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawa tsakanin Bush da Olmert

November 14, 2006

Rikicin gabas ta tsakiya shi ne aka mayar da hankali kansa a ganawa tsakanin Bush da Olmert

https://p.dw.com/p/BtxQ
Bush da Olmert
Bush da OlmertHoto: AP

A haduwa ta karshe da aka yi tsakanin P/M Isra’ila Ehud Olmert da shugaba George W. Bush a fadar mulki ta White House kome ya kasance yana tafiya daidai yadda suke sha’awa a yankin gabas ta tsakiya. Amma fa a tsakanin wancan lokaci zuwa yanzu al’amura sun canza suka dauki wani sabon salo. A dai wancan lokaci P/M Olmert ya gabatar da shirinsa na janyewa daga yammacin kogin Jordan a yayinda shi kuma shugaba Bush ke buga kirji da abin da yake gani tamkar gagarumar nasara ce a gare shi dangane da kafa wata tsayayyar gwamnati ta farko a kasar Iraki. A wancan lokacin kazalika an yi zaton cewar kasar Iran zata ba da kai bori ya hau ga matsin lamba ta kasa da kasa domin ta kakkabe hannuwanta daga shirinta na makamashin nukiliya. Amma fa a halin yanzu tuni murna ta koma ciki. Domin kuwa a hakikatal-amari ita kasar Iraki tana fama ne da yakin basasa a yayinda a Lebanon ake fuskantar barazanar rushewar gwamnatin juyin-juya halin kasar da karfafa angizon kungiyar Hizballah sakamakon wata hadin guiwa tsakanin gaggan daulolin yankin guda biyu, wato Siriya da Iran. Wannan ci gaba kuwa abu ne mafi muni ga Amurka da Isra’ila, kuma ba a hangen wata kafa ta ficewa daga wannan mawuyacin hali na kaka-nika-yi. Amma kuma nuna azama da karfin hali ka iya taimakawa, kamar dai yadda lamarin ya kasance lokacin da shugaba Bush ya bayyana goyan bayansa ga kafa wata ‘yantacciyar kasa ta Palasdinu a shekara ta 2002 ko kuma aiwatar da shirin janyewar Isra’ila daga zirin Gaza da Ariel Sharon, magabacin Olmert yayi a shekara ta 2003. A daidai wannan lokacin da Palasdinawa ke kokarin kafa wata gwamnati ta hadin guiwa tsakanin Fatah da Hamas, Olmert ka iya yin amfani da wannan dama domin tayin shawarwari da sabuwar gwamnatin da za a girka. Kazalika yana iya sake ba da kafar tura kudade zuwa yankunan Palasdinawan da Isra’ila da dora hannu kansu, akalla domin nuna wani hali na sanin ya kamata. A bangaren Amurka kuwa, shugaba Bush na iya gabatar da tuntubar juna da kasar Siriya, kamar yadda hukumar bitar manufofin Iraki dake karkashin jagorancin tsofon sakataren harkokin waje James Baker ta ba da shawara bisa manufar janyo hankalin shugaba Assad ya dawo daga rakiyar kasar Iran. Abin da zai taimaka a nan shi ne taimakawa wajen sasanta tsakaninta da Isra’ila da kuma janyewar Isra’ilar daga tuddanta na Golan, wanda ta haka ita kanta Isra’ilar zata sha fa wa kanta lafiya. Ko da yake hakan ba zai kawar da dukkan matsalolin yankin gabas ta tsakiya fa, amma akalla Isra’ila da Amurka zasu samu wata ‘yar sararawa. Amma ci gaba akan halin da ake ciki yanzun ko kadan ba alheri ba ne ga kasashen biyu. Bugu da kari kuma tun bayan nasarar da jam’iyyar democrats ta samu shugaba Bush ba ya da wata dama ta cin karensa babu babbaka a saboda haka tilas ne ya rika sara tare da duban bakin gatari dangane da manufofinsa na ketare.