1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawa tsakanin Cameron da Obama

Umaru AliyuJuly 21, 2010

Amirka da Ingila sun ƙuduri aniyar haɗa ƙarfi domin magance matsalar tsiyayar mai a tekun Mexiko

https://p.dw.com/p/OQXv
Barack Obama da David CameronHoto: AP

Firaministan Birtaniya David Cameron, ya kai ziyara farko Amirka, tun bayan da ya hau wannan muƙami.A tattanawar da ya yi da shugaba Barack Obama, Cameron ya mussanta zargin  da akewa kamfanin haƙar mai na Birtaniya wato BP ,da hannu  a cikin belin  Abdel Baset al-Megrahi, ɗan ƙasar Libya, wanda a ka samu da lefin tarwatsa jirgin sama a sararin samaniyar Lockerbie a shekara 1988.

A ɗaya hannun, shugabannin biyu sun tattana game da ƙoƙarin tushe rijiyar man kamfanin BP da ke tsiyaya a tekun Mexiko. David Cameron ya ba Amirka haƙuri game da abinda ya faru , sannan ya buƙaci fadodin Washington da na London, su ƙara haɗa ƙarfi domin magance wannan al´amari.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Umaru Aliyu