1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawa Tsakanin Chirac da Schröder a Paris

May 13, 2004

A ganawarsu a birnin Paris shugabannin kasashen Jamus da Faransa sun yi Allah Waddai da kisan dan-Amurka da aka yi a Iraki da kuma yadda sojojin Amurka suka rika azabtar da fursinonin yaki a gidajen kurkuku

https://p.dw.com/p/Bvjc
Chirac da Schröder
Chirac da SchröderHoto: AP

Schröder da Chirac sun bayyana takaici da kaduwa a game da kisan da aka yi wa wani dan kasar Amurka farar fula a Iraki da kuma yadda sojojin Amurka suka rika cin mutuncin fursinonin yakin da suka tsare a kurkukun Abu Ghoraib. Chirac ya ce fede dan kasar Amurka Nicholas Berg da aka yi wani mataki ne na rashin imani, wanda ya samo asalinsa a zamanin jahiliyya. Shima Schröder ya bayyana kaduwarsa sannan ya mika sakonsa na jaje ga dangin marigayin da kaddara ta rutsa da shi a hannun wasu dakarun sa kai a Iraki. Dukkan jami’an siyasan biyu sun yaba da yadda Amurka ke tallafar laifukan cin zali da azabtar da fursinonin yaki da ake zargin sojojinta da aikatawa. Tantance wannan danyyen aiki da kuma hukunta masu laifukan wani bangare ne na shikashikan mulkin demokradiyya in ji Schröder. A lokacin da suke hira da manema labarai bayan ganawar tasu a birnin Paris, inda suka mayar da hankali akan matsaloli iri dabam-dabam dake addabar duniya a maimakon alakar kasashen biyu, kamar yadda aka saba a zamanin baya, Chirac da Schröder sun shiga rufa-rufa a game da tambayar da aka fuskance su da ita dangane da makomar hadin kan turai. A taron kolin da shuagabannin kasashen KTT zasu gudanar a Brussels tsakiyar watan yuni mai zuwa dukkan shuagabannin biyu na fatan ganin an tsayar da wata takamaimiyar shawara a game da daftarin tsarin mulki bai daya tsakanin kasashen kungiyar. Schröder ya ki yayi bayani a game da abin da zai biyo baya idan har wasu kasashe kamar Birtaniya suka ki amincewa da daftarin tsarin mulkin, inda ya ce ba ya tsammanin akwai wata kasa da zata yi fatali da wannan muhimmin kundin da zai yi jagora zuwa ga hadin kan kasashen Turai karkashin tuta guda. Ko shakka babu dai a game da cewar a nan Jamus dukkan majalisun dokoki da ta gwamnoni zasu albarkaci kundin. Amma a can Faransa shugaba Chirac na dada fuskantar matsin lamba a game da kada kuri’ar raba gardama, wacce ka iya sanyawa murna ta koma ciki akan manufa. Majiyoyi masu nasaba da majalisar hadin kan manufofin tsaro tsakanin Jamus da Faransa sun ce kasashen biyu zasu dauki nauyin rundunar kiyaye zaman lafiya ta Turai a kasar Afghanistan tun daga watan agusta mai zuwa, inda dukkansu biyu zasu ba da gudummawar sojoji sama da dubu daya a tsakanin sojojin kasashen Turai kimanin dubu biyar da za a tura zuwa Afghanistan. A karshe Schröder ya mika godiyarsa ga shugaban Faransa Jaques Chirac wanda ya gayyace shi zuwa Normandie domin halartar bikin samun shekaru 60 da kutsawar askarawan taron dangi zuwa wannan yanki a ranar shida ga watan yunin shekarar 1944.