1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawa Tsakanin Fischer Da Gül

October 19, 2004

A ziyararsa ta yini biyu ga Berlin ministan harkokin wajen kasar Turkiyya ya gana da takwaransa ministan harkokin wajen Jamus, inda suka yi musayar rayu a game da maganar karbar Turkiyya a Kungiyar Tarayyar Turai

https://p.dw.com/p/BvfS
Ministocin harkokin wajen Jamus da Turkiyya
Ministocin harkokin wajen Jamus da TurkiyyaHoto: AP

A baya ga wakilan gwamnati, ministan harkokin wajen kasar ta Turkiyya Abdallah Gül ya tsayar da shawarar ganawa da wakilan ‚yan hamayya na jam’iyyun Christian Union, wadanda suka fito fili suna masu bayyana kyamarsu ga karbar Turkiyyar a Kungiyar Tarayyar Turai. An dai saurara daga bakin ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer yana mai bayanin cewar kasar zata ba da cikakken goyan baya ga Turkiyya lokacin da za a tsayar da shawara ta karshe game da kama shawarwari da ita a zauren taron kolin shuagabannin kasashen kungiyar ta tarayyar Turai a cikin watan desamba mai zuwa. Ya ce wannan maganar tana da muhimmanci kuma wajibi ne kasar Turkiyya a nata bangaren ta ci gaba da namijin kokari a matakanta na garambawul. A baya ga haka ministan harkokin wajen na Jamus yayi suka da kakkausan harshe a game da cece-kucen da ake yi a nan kasar sakamakon shawarar da hukumar zartaswa ta KTT ta bayar dangane da fara shawarwarin karbar kasar Turkiyya. Da farkon fari dai shuagabannin jam’iyyun Christian Union sun kuduri niyyar gabatar da wani mataki na shawo kan jama’a domin adawa da wannan manufa, amma daga bisani sai suka canza shawara sakamakon tofin Allah tsine da aka rika yi game da matakin nasu. A lokacin da ya tabo wannan batu ministan harkokin waje Joschka Fischer karawa yayi da cewar:

Duk wanda ya saurari wannan cece-kuce zai yi zaton cewar ba batu ake yi game da shiga shawarwari da Turkiyya ba, magana ce da ta shafi shawarar karbarta nan take. Amma fa abin dake akwai shi ne biyayya ga shawarar da hukumar zartaswa ta KTT ta bayar sakamakon ci gaban da Turkiyya ta samu a karkashin ka’idojin yarjejeniyar Kopenhagen, bayan shekaru 40 da kasar tayi tana fafutukar shigowa inuwar kungiyar.

Shi ma ministan harkokin wajen Turkiyya Abdullah Gül ya tabo wannan dari-dari da kasashe da dama na KTT ke yi game da karbar kasar, inda ya ce lokaci bai yi ba da za a gabatar da wata kuri’a ta raba gardama akan wannan batu. Da farko wajibi ne a fara gabatar da shawarwarin karbar tukuna, kuma wannan lamari ne da zai dauki lokaci mai tsawo ana gudanar da shi. Wannan ziyarar ta ministan harkokin wajen kasar ta Turkiyya tana da nufin share fage ne ga wata ganawar da aka shirya gudanarwa tsakanin P/M Turkiyya Erdogan da shugaban gwamnatin Jamus Schröder da kuma shugaban kasar Faransa Chirac a birnin Berlin mako mai zuwa. A ganawar tasu za a mayar da hankali ne ga adawa mai tsananin da ake fuskanta a kasar Faransa a game da maganar karbar Turkiyyar a KTT.