1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawa tsakanin Hamas da mahukuntan Rasha

March 3, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6B

A yau tawagar shugabannin Hamas suka isa birnin Mosco domin tattaunawa da mahukuntan ƙasar Rasha, a wani mataki na neman goyon bayan kasashen duniya.

Wata sanarwa daga ƙungiyar ta Hamas ta ce tawagar mai wakilai shidda dake karkashin jagorancin Khaleed Meshaal za su gana da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da kuma wasu ƙusoshin gwamnatin Rasha.

Baá bada sanarwar ko tawagar za ta gana da shugaban ƙasar Rashan Vladimir Putin ba. kasar Rasha dai na ɗaya daga cikin manyan ƙasashe dake shiga tsakani domin samar da wanzuwar zaman lafiya a gabas ta tsakiya ƙarkashin daftarin nan na road map. Bisa wannan ganawa dai, Rasha ta kasance ƙasa ta farko da zata yi tattaunawa ta kai tsaye da Hamas, tun bayan da ta karbi ragamar iko a yankin Palasɗinawa. Hamas ta sami nasara a zaɓen majalisun dokokin Palasɗinawa da ya gudana a watan Janairu wanda ya zamanto ba zata ga kasashen duniya. Ita ma dai ƙasar Rasha ta yi kira ga Hamas ta dakatar da tarzoma ta kuma amince da wanzuwar ƙasar Israila.