1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawa tsakanin Schröder da Bush

June 28, 2005

A jiya litinin shugaba Bush na Amurka ya karbi bakoncin shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder a fadar mulki ta White House

https://p.dw.com/p/Bvb3
Schröder a kofar fadar mulki ta White House
Schröder a kofar fadar mulki ta White HouseHoto: AP

Ganawar dai ta gudana a karkashin wani kyakkyawan yanayi, inda aka lura da sararawa a fuskokin shuagabannin biyu. Mai yiwuwa wannan ganawar ta ban-kwana ce, saboda a wannan marra da ake ciki yanzun ba wanda ya san yadda zata kaya a zaben shugaban gwamnati da majalisar dokoki ta Bundestag da ake da niyyar gudanarwa nan gaba a wannan shekara. Al-Ayyi-halin dai wannan ganawar tana mai yin nuni ne da sararawar al’amura da aka samu a dangantakar kasashen Amurka da Jamus, bayan zaman dardar da aka fuskanta tsakaninsu sakamakon yakin Iraki misalin shekaru uku da suka wuce. Wani abin dake yin nuni da kusantar junan da aka samu shi ne yadda shugaba Bush ya koma ga kiran shugaban gwamnatin Jamus da sunansa na yanka, wato Gerhard, a mai makon takensa na shugaban gwamnati, wato Chancellor. Dukkan shuagabannin biyu sun tattauna muhimman matsalolin da suka shafi dangantakar kasa da kasa, tsakani da Allah ba tare da wata rufa-rufa ba. Kama daga kaunar da Jamus take yi ta samun dawwamammiyar kujera a kwamitin sulhu na MDD zuwa ga hulda da shuagabannin kasar Iran. Wani abin da aka lura da shi a game da bukatar kujera ta dindindin da Jamus ke yi a kwamitin sulhu na MDD shi ne kasancewar tayi gaban kanta ne tana mai neman goyan baya daga sauran kasashe a maimakon dogara kacokam akan kasar Amurka. Schröder yana sane da cewar, a bisa wasu dalilai, kasar ta Amurka tana dari-dari da maganar bai wa Jamus dawwamammiyar kujera a kwamitin na sulhu. A sakamakon haka shugaban gwamnatin na Jamus bai dadara ba yana mai fafutukar neman goyan baya daga sauran kasashe, kafada-da-kafada da kasashen Japan da Indiya da kuma Brazil, wadanda su ma suke neman samun irin wannan kujera. Za a ga sakamakon wannan yunkuri nasu akalla a cikin watan satumba mai zuwa lokacin taron babbar mashawartar MDD.

Dangane da maganar Iran kuwa, Amurka na neman goyan baya daga Jamus da sauran kasashen KTT a kokarin shawo kann takaddamar da ake yi akan shirin kasar ta Iran na tashar makamashin nukiliya. Domin kuwa a halin da muke ciki yanzu haka Amurka ba zata kuskura ta nemi tinkarar rikicin da karfin hatsi ba. Kazalika kasar ta Amurka tana bukatar goyan bayan Jamus a fafutukar samar da zaman lafiyar kasar Afghanistan. Ita dai gwamnatin shugaba Karzai tana cikin mawuyacin hali na kaka-nika-yi game da makomarta kuma sai tare da taimakon kungiyar tsaro ta NATO ne gwamnatin zata iya tsallake rijiya da baya domin yada angizonta zuwa sauran sassa na kasar Afghanistan. A can Irak kuwa, Jamus na ba da cikakken goyan baya wajen ba da horo ga jami’an tsaron kasar a kokarin tabbatar da mulkin demokradiyya a cikinta.

A lokacin ganawar tasu tare da shugaba Bush Schröder yayi wa shugaban Amurkan hannunka mai sanda dangane da wani ci gaban da ya dade yana ci masa tuwo a kwarya. Wannan maganar ta wani abin da aka kira ne wai Hedge-Fonds, wanda ake amfani da kudadensa domin sayen kamfanonin Jamus. Schröder ya ce sassaucin ciniki da gasar kasuwanci, wata manufa ce dabam, amma ba zata yiwu kasa ta zauna sasakai tana mai zura ido akan masu kokarin yin tasiri akan tattalin arzikinta daga ketare ba. Ita kanta. Ita kanta kasar Amurka, wannan ci gaba na ci mata tuwo a kwarya, ganin yadda kamfanonin kasar China ke kokarin handume kamfanonin Amurka ba ji ba gani. Mai yiwuwa a samu hadin kai tsakanin Amurka da Jamus domin dakatar da wannan ci gaba duk da goyan bayan da dukkansu ke bayarwa ga kusantar tattalin arzikin kasa-da-kasa. A takaice dai shugaba Bush ya taka tasa rawar wajen kyautata makomar dangantaku tsakanin Amurka da kasashen Turai, a nasu bangaren tilas ne Jamusawa su yi taka tsantsan ka da su yarda wata manufa ta kyamar Amurka ta dabaibaye matakansu na yakin neman zaben da ake da niyyar gudanarwa a kasar nan gaba a wannan shekara.