Ganawa tsakanin tawagogin Amurika da na Korea ta Arewa
March 6, 2007An fara ganawar ƙut da ƙut tsakanin tawagogin Amurika da na Corea ta Arewa, a game da rikici makaman nuklea.
A wannan tantanawa wadda utace ta farko, tun shekaru 6 da su ka gabata, ƙasashen2, na ɗauke da burin cimma matakin dindindin, na kai ga warware wannan taƙƙaddama.
Shugaban tawagar Corea ta Arewa, Kim Kye-Gwan, ya gana da ƙurraru ta fannin nuklea, kamin ya sadu da shugaban tawagar Amurika, Christopher Hill.
Bayan wata da wattani, a na kai ruwa rana, a kan wannan rikici, a ƙarshe dai, Corea ta Arewa, ta amince da yin watsi, da aniyar mallakar makaman nuklea, tare da gitta sharaɗin ƙasashe masu shiga tsakani, su taimaka mata, wajen haɓɓaka tattalin arziki.
A ɗaya wajen kuma, yau ne wata tawagar ƙungiyar tarayya Turai ta sauka, a birnin Pyong Yang,inda ita ma, zata tantana wannan batu, tare hukumomin ƙasar.