1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Ƙungiyar Tarayyar Turai da Rasha.

May 31, 2010

Yau ake fara taron koli na Ƙungiyar Tarayyar Turai(EU) da Rasha.

https://p.dw.com/p/NeDO
Hermann van Rompuy, shugabar Ƙungiyar Tarayyar Turai(EU).Hoto: AP

A yau shugabannin Ƙungiyar Tarayyar Turai da na ƙasar Rasha ke gudanar da wani taron koli da ake sa ran cewa zai fi mai da hankali akan matsalar tattalin arziƙi da ke addabar ƙasashe masu amfani da kuɗin euro. Da farko, Shugaba Dmitry Medvedev na Rasha da shugaban Ƙungiyar Tarayyar Turai, Hermann van Rompuy za su shiga wata liyafa a garin Rostov on Don. Wannan shi ne karon farko da van Rompuy ke ziyara a ƙasar Rasha tun bayan ƙirƙirar da wannan muƙami nasa a ƙarƙashin yarjejeniyar Lisbon. Rompuy na kan wannan ziyarar ne tare da Catherine Ashton, kantomar Ƙungiyar Tarayyar Turai kan manufofin ƙetare. Taron zai kuma mai da hankali akan batutuwa da dama kama daga tsamin dangantaka da ake daɗe an fama da shi tsakanin Ƙungiyar Tarayyar Turai da Rasha da kuma batun visa tsakanin ɓangarorin biyu.

Mawallafiya. Halimatu Abbas

Edita: Abdullahi Tanko Bala