1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Abbas da Olmert

Hauwa Abubakar AjejeAugust 6, 2007

A yau ne shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas ya karbi bakuncin firaministan Israila Ehud Olmert a Jericho na yankin Palasdinawa,inda suka tattauna batun samarwa palasdinawa yancinsu.

https://p.dw.com/p/Btuo
Hoto: AP

Ganawara ta gudana ne a birnin Jericho na yankin Palasdinawa,wannan kuma shine karo na farko da wani shugaban Israila zai kai ziyara yankin Palasdinawa cikin shekaru 7.

Firaministan Israila ya baiyana fatar cewa wannan tattauanwa zatayi tasiri ga muhawara kan samarwa da Palasdinu yancin cin gashin kanta.

“ina murnar tarbar da aka mana a Jericho nazo nan ne da nufin tattaunawa da zata kai ga samarda kafa kasar Palasdinawa mai yancin kanta"

Jamian Palasdinawa sunce za’a ci gaba da wannan tattaunawa har zuwa lokacin babban taron kasa da kasa na zaman lafiya nan gaba cikin wannan shekara,wanda shugaban Amurka ya sanar cikin jawabinsa na ranar 16 ga watan yuli.

Babban mai shiga tsakani na Palasdinawa Saeb Erakat gabanin taron yace jamaar palasdinawa suna son ganin sakamako mai maana a taron.

“ jamaa suna son yin anfani da danuwansu ba kunuwansu ba,sun gaji da jinmu.sun gaji da jinmu muna batun zaman lafiya da yiwuwar zaman lafiya ba tare da sun gani a kasa ba.suna bukatar ganin mun samu nasara”

mai magana da yawun Olmert yace shugaban Palasdinawa ya bukaci Olmert day a kara sakin wasu fursunoni Palasdinawa,bayan wasu 250 da aka sako cikin yan makonnin nan.

A makon daya gabata ne dai sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice ta kai ziyara YGTT domin samarda goyon baya ga wannan taro inda ta sanarda cewa Olmert yace a shirye yake ya tattauna kan muhimman batutuwa da zasu kai samarda kasar Palasdinu tsakanisa da shugaba Abbas.

Palasdinawa a nasu bangare sun baiyana fatar magance batun matsayin birnin Qudus da yankunan da Israila ta mamaye a gabar yamma da kogin Jordan,hakazalika da batun yan gudun hijirar Palasdinu da zuriyarsu.

A halinda ake ciki kuma kungiyar Hamas tayi Allah wadai da ganawar ta yau tsakanin Olmert da Abbas tana mai baiyana cewa babu abinda ganawa na baya suka haifar ga jamaar Palasdinu.

Tsohon firaminista Ismail Haniyeh yace irin wannan ganawa kafa ce kawai da ake neman baiwa Amurka domin ta tabbatar da manufofinta na ci gaba da dakushe Palasdinwa tare kuma da kaddamar da sabon yaki kan kasashen musulmi da sauran kasashe na yankin.

Babu dai tabbas ko Olmert wanda martabarsa tayi kasa bayan yakin da basu samu nasara ba a Lebanon ko zai iya wani muhimmin sassauci musamman wajen tunbuke matsunan yahudawa yan share wuri zauna a yamma da gabar kogin Jordan.

Hakazalika babu tabbas ko Abbas zai iya cimma yarjejeniya da kungiyar Hamas dake rike da zirin gaza wadda kuma take kira da lalata Israila.

Kakakin maaikatar harkokin wajen Israila Mark Ragev yace kasarsa tana aiki ne da halaltacciyar gwamnatin Palasdinawa kuma tana son nunwa Palasdinawa cewa zasu iya cin moriyar ababe da dama ta hanyar sasantawa da kasar ta yahudawa.