1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Abbas da Olmert

July 16, 2007
https://p.dw.com/p/BuG9

Prime ministan izraela Ehud Olmert da shugaban yankin palasdinawa Mahmoud Abbas sun fara wata ganawa a birnin Kudus,adangane da shirin da Izraelan keyi na tallafawa gwamnatin yankin dake gabar yamma da kogin Jordan.A mataki na farko dai Izraelan a jiya ta sanar dacewa bazata kaiwa mayakan kungiyar fatah 180 hari ba,idan idan sunyi alkawarin dakatar da kaiwa kasar Izraelanh hari.Gwamnatin Amurka dai na na bukatar Olmert ya sake farfado da tattaunawar sulhu da Shugaba Abbas,bayan da kungiyar Hamas ta karbe madafan iko a yankin Gaza a watan daya gabata.A karshen mako nedai shugaban Palasdinawan ya sanar da sabuwar gwamnati,wadda zata maye gurbin na yan hamas,da aka zaba ashekarar data gabata.