1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Abbas da Sarkozy

September 27, 2010

Nicolas Sarkozy ya ce ƙasashen Turai sun taka rawar gani wajen wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya

https://p.dw.com/p/PO1i
Sarkozy da AbbasHoto: AP
Shugaban Fararansa Nicolas Sarkozy ya ce zai karɓi baƙuncin shugabannin Isra'ila da na Palasɗinu a wata mai kamawa. Sarkozy ya bayyana haka ne a yayin da yake neman ƙasashen turai da ma ƙasashen da ke tekun Bahr - Rum da su taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya a yankin Gabas Ta Tsakiya. Shugaba Sarkozy, wanda a yau ya karɓi baƙuncin shugaba Mahmud Abbas na Palasɗinu, ya nemi ya san makomar tattaunawar samar da sulhu a yankin na Gabas Ta Tsakiya da aka riga aka fara. Ya kuma buƙaci a sake ɗage wa'adin gine-ginen Isra'ila da aƙalla watanni ukku zuwa huɗu. Daga bisani dai Sarkozy ya ce shugaba Abbas, da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da shugaban Masar Hosni Mubarak za su ziyarci birnin Paris a watan Oktoba domin shirye - shiryen wani taron ƙoli na ƙasashen tekun Bahr - Rum da za'a gudanar a watan Nuwamba - idan Allah ya kaimu.

Mawallafiya : Pinaɗo Abdu

Edita:Umaru Aliyu