1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Merkel da shugaban Ukraine

August 30, 2010

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta gana da shugaban Ukraine.

https://p.dw.com/p/OzkV
Merkel da Yanukovich yayin ganawarsu a birnin Berlin.Hoto: picture alliance/dpa

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta tattauna tare da Shugaba Viktor Yanukovich na ƙasar Ukraine. Merkel ta ce, yayin ganawar tasu ta fito ɓaro-ɓaro ta yi magana game da buƙatar tabbatar da 'yancin 'yan jarida a wannan ƙasa . Yan jarida a ƙasar ta Ukraine dai sun daɗe suna hannunka mai sanda game ƙara taɓarɓarewar halin da suka tsinci kansu a ciki,  suna masu cewa tun sanda Yakunovich ya ɗare kan karagar mulki a watan Fabarairu ne,  suke fuskantar matsin lamba.  Merkel ta ƙara da cewa, Jamus na buƙatar ba da ƙarin taimako domin zamanta tsarin aikin iskar gas. Ta ce  Ukraine na taka muhimmiyar rawa wajen samar da gas daga Rasha zuwa sauran ƙasashen Turai. A dai wani lokaci can baya sai da aka samu saɓani tsakanin Ukraine da Rasha da ya kawo cikas ga aikin rabon gas ga ƙasashen Turai. Merkel ta kuma yi alƙawarin ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasar ta Ukraine da Ƙungiyar Tarayyar Turai.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Zainab Muhammad Abubakar