1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Paparoma Benedit na 16 da shugaban cocin katolika na Jamus

March 12, 2010

Paparoma ya yi Allah wadai kan fyaɗe da mallaman addinai ke yi wa ƙananan yara a coci da makarantu

https://p.dw.com/p/MROW
Shugaban cocin katolika na ƙasar JamusHoto: picture-alliance/ dpa

Paparoma Benedit na 16 Ya gana da shugaban 'yan ɗarikar katolika na ƙasar Robert Zollitsch bayan abin kunya nan da ya auku na fyaɗe da aka samu a ƙasar ta Jamus shugabanin adinai na krista akan yara ƙanƙana. Wanan ganawa da a yi ta musamun tsakanin mutane biyu, bayan taro na shekara da aka yi na kiristocin, ganawar tasu ta mayar da hankaline dangane da butun na fyaɗe na malaman addinai na kirista da ya zama abin Allah wadai ko'ina a cikin ƙasashen yammacin Turai. Robert Zollitsch ya ƙara sanar da Paparoma akan abinda ke faruwa a ƙasar ta Jamus dangane da maganar ta fyaɗe a cikin cocinan 'yan katolikan da ake samu.Tun a cikin watan janairu ne dai ake zargin cocin katolika da laifuka na fyaɗe ga yara ƙanana a cikin makarantu. Shugabanin cocin dai sun yi alƙawarin bayar da cikkaken haske dangane da wannan al' amari

Bayan ganawar Robert Zollitsch ya nemi gafara ga waɗanda suka fuskanci lamarin fyaɗe daga malamai addinin a ƙasar ta Jamus, ya kuma ayyana cewa Paparoma ya umarce shi da ya ci gaba da bada himma domin kawo karshen irin wannan aikin asha da ke faruwa a cikin cocinan. Zollitsch ya ce lamarin fyaɗe ba cocinan roman katolika kaɗai ya shafa ba, inda yace magana ce da ta zame ruwan dare.ga dukanin ɗariƙu.

Mawallafi: Abdurahman Hassan

Edita: Halima