1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Wulff da shugabannin EU

July 8, 2010

Sabon shugaban Jamus yana tattauna lamuran da suka shafi Turai tare da shugabannin ƙungiyar EU

https://p.dw.com/p/OEWU
Hoto: AP

Sabon shugaban Jamus Christian Wulff ya nuna cikakken goyon bayan sa ga ƙungiyar Tarayyar Turai a lokacin da ya kai ziyarar sa ta farko a hedikwatar Tarayyar Turai dake birnin Brussels na ƙasar Beljiam. Wulff, wanda ya gana da shugaban Hukumar Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso, ya bayyana buƙatar ƙara sanar da jama'a irin kyawawan ayyukan da Hukumar Tarayyar Turai da kuma Majalisar dokokin ƙungiyar suka gudanar fiye da yadda lamarin yake a yanzu.

Sabon shugaban na Jamus yana kuma ganawa da babban Sakataren ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO Anders Fogh Rasmussen domin jin nazarinsa game da rawar da dakarun ƙungiyar ke takawa a ƙasar Afghanistan, ciki kuwa harda neman sanin wa'adin ƙarawa ko kuma rage yawan dakarun NATOn a ƙasar ta Afganistan.

A jiya Laraba ce dai Wulff ya fara rangadin sa na farko zuwa ƙetare, inda ya kai ziyara ƙasar Faransa game da ganawa da shugaba Nikolas Sarkorzy na ƙasar ta Faransa da kuma kai ziyarar ´ban girma zuwa Majalisar dokokin Tarayyar Turai dake da wani mazauni a Strasbourg.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Yahouza Sadisou