1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin adawa da Amurka a Italiya

February 17, 2007
https://p.dw.com/p/BuRZ

Dubban alummomin kasar Italia ne suka fara gudanar da wani gangami a birnin Vicenza dake arwaci,domin bayyana dawarsu da shirin fadada sassanin dakarun sojin Amurka dake kasar.Tuni dai aka dauki tsauraran matakan tsaro a kewayen sansanin dakarun sojin,domin gudun kada sojojin sakai su dauki wannan dama wajen kaiwa sansanin hari.Washinton dai na shirin kaurar da dakaru kimanin dubu 2 ,wadanda a halin yanzu ke nan Jamuzs zuwa headquatarsu dake Italiya,wanda zai kaweo ga dadain dakarun amurka a vicenza zuwa kimanin dubu 5 kenan.Wannan shirin fadada dakrun Amurka a Italiyan dai ya na neman jefa jammiyar prime minista Romano Prodi cikin wani wadi na tsaka mai wuya.