1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin makiya da masoyan baki a Jamus

Mouhamadou Awal Balarabe/USUOctober 20, 2015

Dubban magoya bayan kungiyar Pegida ta masu kyamar musulmi da baki suka gudanar da gangami a gabashin kasar domin nuna adawarsu da kwararar 'yan gudun

https://p.dw.com/p/1Gr5s
Dresden - Pegida-Anhänger versammeln sich zum Jahrestag
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Hirschberger

Rundunar 'yan sandan Jamus ba ta bayyana yawan masu kyamar baki da suka halarci gangamin cika shekara guda da kafa kungiyar ta Peguida. Kafofin watsa labaran kasar sun kiyasta cewar, wadanda suka gangamin sun kai dubu 15 zuwa 20, adadin da ya ja baya idan aka kwatanta da mutane dubu 25 da suka halarci gangamin da kungiyar ta gudanar a watan Janairun bana.

Da yawa daga cikinsu dai na dauke da kwalaye masu dauke da rubutun batanci ga shugabar gwamnatin kasar ta Jamus Angela Merkel, wacce suke zargi da bude kofofin kasar ga baki musmman ma 'yan gudun hijira. Sannan kuma sun ta kada tutar Jamus tare da bayyana cewar ba abin da baki 'yan gudun hijirar Siriya da kuma Iraki kuma musulmai za su iya karawa Jamus, illa jefa ta cikin ayyukan ta'addaci.

Ko da wata dattijuwa da ke halartar ganganmi na Peguida, sai da ta ce bisa ga abin da aka tsegunta mata, akidar kisa ce kawai ake cusawa musulmai a cikin masallatai, saboda haka ne ba ta yarda da su ba.

"Idan mutun ya yi ko yi da zane-zane a cikin masallaci, to dukkaninsu musulunci binsa suke yi da wuka. Wani ne ya gayamin a yau din nan."

Sai dai kuma dan jaridar da yake yi wa mata tambaya da Jamusanci, dan asalin yankin larabawa ne. Saboda hake ne shi Ja'afar Abdul Karim ya tambayeta ko ta na tsoron shi, sai ta ce

"A a . sam-sam bana tsoronka. kai ka riga ka saje. Wannan ya na nufin cewar ka riga ka nakalci al'adun Jamusawa."

Shi dai Ja'afar Abdul Karim ya na daya daga cikin wadanda suka jikkata a gangamin na masu kyamar baki da musulmi a Dresden. To ko ya aka yi har wannan tashin hankali ya ritsa da shi?

"Ja'afar ya ce muna tsaka da aikinmu a matsayin 'yan jarida, inda muke tambayar 'yan Peguida dalilan su na yi wannan gangami da kuma me ya sa suke jin tsoron musulmi, sai wasu gungunsu suka fara ce mun bace daga nan, ka daina yi mana tambayoyi, kai makaryaci ne. Daga bisani ni kuma suka fara ture ni, wasu matasa daga cikinsu suka buge ni a bayan wuya ta."

Da ma dai 'yan sandan kwantar da tarzoma sun ja daga domin hana barkewar tashin hankali tsakanin masu kyamar baki da kuma masu goyon bayan manufofin gwamnatin Merkel.

A gefe guda kuma wasu Jamusawa kimanin dubu 14 ne suka gudanar da nasu gangamin domin kalubalantar masu kyamar bakin, inda suka yi ta kira ga al'umma da su ci gaba da bude kofofinsu ga 'yan gudun hijira.

A yanzu haka dai ra'ayin Jamusawa a kan batun 'yan gudun hijira. Akwai wadanda suke na'am da yunkurin shugabar gwamnati Angela Merkel na ci gaba da tarbar 'yan gdun hijira. Sannan kuma akwai masu mara wa Peguida baya suna masu cewar bakin za su mamaye gurabensu na aiki da kuma gidanjensu.

Ita dai kungiyar ta Pegida ta fara mayar da hankali ne a kan kyamar kudin Euro a lokacin da aka kirkirota saboda illar da suka nunar da wannan takardar kudin ke yi ma tattalin arzikinsu. Daga bisani ne kungiyar ta rikida i zuwa ta nuna tantagariyar adawa da duk wasu manufofi da suka shafi Islama a kuma Muslmi a tarayyar Jamus.

Dresden Anti Pegida Demonstration Die Grünen
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Hiekel
Dresden Kundgebung Pro Einwanderung Anti Pegida Demonstration 10.01.2015
Hoto: picture-alliance/dpa/Arno Burgi