1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Leitartikel: Jenseits aller Statistik

September 30, 2010

Shekaru 20 kamar ƙiftawa ne da Bisimilla a cikin tarihi. Wajibi ne kuma masu ƙoƙarin yin amfani da kewayowar shekaru ashirin da sake haɗewar Jamus domin ƙorafi akan banbance-banbancen dake akwai, in ji Marc Koch.

https://p.dw.com/p/POb3

Alƙaluma dai su ne ke taka muhimmiyar rawa dangane da wannan biki. Bayanai da ƙididdigar dake ba da haske a game da matsayin Jamus a yau bayan shekaru 20 da sake haɗewar ta. Haƙƙun ne cewar da yawa daga cikin waɗannan ƙididdigar na yin nuni ga wasu kurakurai da aka yi a cikin shekaru 2o da suka wuce da kuma cewar har yau akwai rashin adalci, inda yawan marasa aikin yi a gabacin Jamus ya ninka na yammaci har sau biyu kuma ma'aikata a yammaci sun fi takwarorinsu a gabacin ƙasar samun albashi mai tsoka. Dukkan waɗannan abubuwan mutum zai iya bitarsu a bincike daban-daban da aka gudanar a kkimiyyance. Amma wani bayani ne dukkan waɗannan abubuwan ke bayarwa game da Jamus da sake haɗewar ƙasar? A haƙiƙa ba wani abu ne da ya taka kara ya karya ba.

Abin mamaki a cikin tarihi

Shiri mafi girma da aka gabatar wanda kuma har yau ba a kawo ƙarshensa ba a cikin tarihin Jamus na bayan yaƙin duniya na biyu ba zai lissaftu a ƙididdige ba. Ko shakka babu mazauna yankin tsofuwar janhuriyar yammacin Jamus na fama da raɗaɗin nauyin dake kansu, wanda ya haddasa tura dubban miliyoyin kuɗi na Euro zuwa gabacin ƙasar ake kuma ci gaba da turawa har ya zuwa halin da muke ciki yanzu. Amma ƙalubale mafi girma shi ne yadda ala tilas mazauna tsofuwar ƙasar Jamus ta Gabas su canza salon rayuwarsu sakamakon wargajewar tsarinsu na zamantakewa da siyasa da kuma tattalin arziƙi.

Sai dai kuma jama'a basu martaba nasarorin da aka samu. A maimakon haka sai ƙorafi ake yi ba ƙaƙƙautawa – ko da shi ke waɗannan ƙorafe-ƙorafe bayan shekaru 20 ba kome ba ne face neman wata maslaha ta siyasa. Ya Alla a gabaci ne ko a yammaci. Domin kuwa ba wanda zai yi tsammanin cewar a cikin shekaru ashirin kacal ƙasashe biyu da tsare-tsaren zamantakewarsu suka yi daura da Juna kamar Jamus ta Yamma da Jamus ta Gabas zasu saje gaba ɗaya ba tare da wani giɓi ba. Duk wanda ke buƙatar ganin cewar, a yai shekaru 20 bayan haɗewar, ba wani banbanci tsakanin gabaci da yammaci, to kuwa bai fahimci girman alƙiblar da aka fuskanta a cikin wannan manufa ta tarihi ba.

Babu lokaci na gwaje-gwaje

Kuma gaskiyar cewa an caɓa kurakurai da dama tsakanin faɗuwar katangar Berlin da ranar uku ga watan oktoba na 1990 tare da rashin tantance al'amura da idanun basira, ba zata canza kome ba. Abin dake akwai yau shi ne: Masu tsara manufofin sake haɗewar Jamus a wancan lokaci bas u da wata cikakkiyar dama ta yin gwaje-gwaje, ba lokaci na neman kusantar juna sannu a hankali tsakanin ƙasashen Jamusawan guda biyu. Ya zama wajibi akansu su yi amfani da wannan dama ta tarihi da ta samu a daidai lokacin da ake samun tsauraran canje-canje ga tsarin dangantakun ƙasa da ƙasa. Ko shakka babu an yi garaje wajen yi wa mutane alƙawarin cewa haɗewar zata tabbata a cikin wasu shekaru ‘yan ƙalilan ba kuma tare da an kasha wasu kuɗaɗe masu yawa ba, kamar yadda tsofon shugaban gwamnati Helmut Kohl yayi a shekara ta 1990. Har yau ana amfani da wannan maganar tamkar wata hujja a mahawarorin da akan gudanar. Sai dai hakan ba zai tauye martabar Kohl da sauran waɗanda suka taka muhimmiyar rawa wajen sake haɗewar ba.

Domin kuwa Jamus ta ci moriyar sake haɗewar ta kowace fuska. Daga ciki kuwa hard a kasancewar ƙasar ta buɗe ƙofofinta tana mai ƙunshe da al'adu iri daban-daban kuma cike da rayuwa a tsakanin waɗannan shekaru 20. Ta koyi dabarun ɗinke dukkan ɓaraga da kan samu a tsakanin jama'a a zamantakewarsu ta yau da kullum a maimakon yin ko oho da lamarin. Ƙasar ta daina lalube a cikin duhu a maimakon haka tana amfani ne da kaifin ido domin tinkarar matsaloli. Tuni Jamus ta zama tamkar wani ɗakin binciken kimiyya a tsakiyar nahiyar Turai, inda take da ikon fuskantar canje-canje da sabbin ƙalubale da kuma amfani da basira. Dukkan waɗannan abubuwa sun samu ne sakamakon sake haɗewar ƙasar. Kuma wannan bayanin ya fib a da haske game da halin da ƙasar ke ciki fiye da wata ƙididdigar da za a bayar.

Mai fassara: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal