1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Garambawul ga majalisar ministoci a Nijeriya

Ubale MusaOctober 30, 2008

An dai daɗe ana jiran shugaban Nijeriya da ya yiwa majalisar ministocin wannan garambawul.

https://p.dw.com/p/FkEm
Majalisar dokokin Nijeriya a AbujaHoto: DW

Da yammacin ranar Laraba 29 ga watan Oktoban shekara ta 2008, shugaban tarayyar Nijeriya Umar Musa ´Yar Adua ya sanar da yiwa majalisar ministocin gawambawul, matakin da aka daɗe ana jiran ya aiwatar a ƙasar ta Nijeriya mai arzikin man fetir. Wannan garambawul na farko da fadar shugaban ƙasa a Aso Rock ta yi ya shafi ministoci 20 na gwamnatin shugaba ´Yar Adua.