1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Garambuwal a ministocin Nijar

Usman Shehu Usman
October 20, 2016

Shugaba Mahamadou Issoufou ya yi wa gwamnatinsa garambawul inda ya bai wa wasu 'yan adawar kasar kujeru shida a cikin majalissar ministoci mai mambobi 42

https://p.dw.com/p/2RUCM
Niger Amtseid des neu gewählten Präsidenten Mahamadou Issoufou
Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Sai dai kusoshin tsohuwar gwamnatin sun ci gaba da zama a cikin sabuwar majalisar ministocin, inda alal misali ministan cikin gida Mohamed Bazoum ya ci gaba da kasancewa kan kujerarsa, a yayin da Hassoumi Massaoudou tsohon ministan tsaro ya samu mukamin ministan ma'aikatar kudi ta kasa. 

A yayin da ministan kiwon lafiya Kalla Moutari ya maye gurbin Hassoumi Massaoudou a kan harakokin tsaron. Ministan ma'aikatar man fetur Foumakoye Gado ya ci gaba da zama kan mukaminsa. 'Yan adawa shida da suka samu mukami a cikin sabuwar gwamnatin sun hada da Malam Almoustapha Garba da Illiassou Idi Mainassara daga jam'iyyar MNSD Nasara. 

Shugabannin jam'iyyun da suka dafawa shugaban kasa a lokacin zaben watan Febrarun da ya gabata, ko wannensu ya ci gaba da zama a cikin sabuwar majalisar ministocin gwamnatin kasar.