1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

GARGUKUWA DA DALIBAN MAKARANTA A RASHA.

September 1, 2004

Wasu yan ta kife sun yi garkuwa da dalibai a wata makaranta dake kudancin Rasha.

https://p.dw.com/p/Bvgr
Shugaba Vladimir Putin na Rasha.
Shugaba Vladimir Putin na Rasha.Hoto: AP

Wasu yan kunar bakin wake,daure da jigidfan boma bomai sun cafke wata makaranta a wata gunduwar Rasha dake kann iyaka da Lardin Checchiniya,inda suke cigaba yin garkuwa da daruruwan mutane,da suka hadar da Daliban makarantan 200.

Wannan harin nayau daya ritsa da wannan makaranta,yazo ne yini guda bayan harin kunar bakin wake da wata mace tayi daya kashe akalla mutane 10 banda wadanda suka tagayyara a birnin Moscow.

Ya zuwa yanzu dai an tabbatar dacewa mutane 2 suka rasa rayukansu a harin na yau,wadanda suka hadar da baban wani Dalibi daya kawo dansa makaranta,da daya daga cikin masu harin,banda mutane 9 da suka samu raunuka.

Harin na yau dai yazo ne dai dai da bukin ranar farkon shekarar koyarwa a makarantun Rasha,inda rahotanni ke nuni dacewa,akasarin iyayen Daliban sun dawar da yayansu makaranta a safiyar yau din.

Yan kunar bakin waken dai sunyi barazanar tayar da boma bomai da suke daure dasu,idan har yansanda sunyi yunkurin shiga makarantar,ayayinda suka tilastawa Daliban tsayawa a jikin tagogin ajujuwansu.,ata bakin kakakin Yansanda dake kudancin Rashan.

Duk dacewa babu wata shaida kai tsaye dake nuna halaka tsakanin harin jiya a birnin Moscow dana a yau a kudancin kasar,akwai zargin hannun yan tawayen Checchiniya,ko kuma masu mara musu baya.

Wadannan hare hare guda biyu sun auku ne mako guda bayan ,jiragen saman Rashan biyu dauke da pasinja 90 sun fadi kusan alokaci guda,wanda jamiai suka danganta da harin yan taadda.

Ministan tsaro na Rasha Seigei Ivanov,yayi bayanin cewa wannan yaki ne aka kaddamar akansu kai tsaye ,inda baa ganin abokin adawa,balle asan inda ya sa gaba.Bugu da kari wadannan hare hare ba zasu kasa nasaba da kokarin dakushe goyon bayan fadar gwamnatin Kremlin wa zaben shugaban kasa daya gudana ranar Lahadi a Checchiniya ba.A ranar 9 ga watan mayu ne dai aka kashe tsohon shugaba Akhmad Kadyrov,tare da wasu mutane 20 a harin boma bomai.

Bayan yan ta kifen sun mamaye wannan makaranta,anji karar harbin bindigogi ,inda akalla malamai 3 da yansanda 2 suka samu raunuka.Kakakin yansandan yankin ya sanar dacewa akasarin yan harin na daure ne da belt dake dauke da boma bomai na kunar bakin wake,wanda ke nufin duk wani yunkuri na afka musu,ka iya haddasa tayar dasu.

Masu harin dai sun bukaci tattaunawa da jamian yankin,da wani sanannen mutumin daya tallafawa wadanda akayi garkuwa dasu a gidan rawa a Rasha a shekarar 2002,Leonid Roshal.A wancan harin akalla mutane 129 suka rasa rayukansu,daga cikinsu kuwa harda masu kai harin 41.

Rahotannin kafofin yada labarun Rasha sun bayyana cewa akalla Dalibai 50 ne suka samu tserewa.Ajiya kuwa wata mace yar kunar bakin wake ta tayar da Bomb dake jikinta a wata tashar Moscow dake da cunkoson Jamaa,inda nan take mutane 10 suka mutu,banda wau 50 da suka tagayyara.Wadanda suka ganewa idanunsu hadarin sunce ,yar kunar bakin waken na tafiyarta a wannan titi kafin ta hango yansanda suna binciken takardun kowane mai wucewa,nan take saita sauya hanya,inda bomb da take dauke dashi ya tarwatse.

Wata kungiya da take kiran kanta Islambouli Brigade,ta yanar gizo gizo ta dauki alhakin kai wannan hari na jiya,kuma hakan na zama abun alfahari wa goyon bayansu wa musulmin Checchiniya.

Sakamakon wadannan tashe tashen hankula ne yasa,shugaba Vladimir Putin ya katse hutunsa dayakeyi a Sochi,inda ya komo Moscow da gudanar da taron gaggawa da jamian maaikatar harkokin cikin gida dana tsaro.Yanzu dai jamaar Rasha na rayuwa cikin fargaba dangane da wadannan hare hare.

Zainab Mohammed.