1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Garkuwa da babban jami'in Jamus a kasar Yemen.

December 30, 2005

Jami'an ma'aikatar harkokin wajen Jamus a birnin Berlin na nan na ta kokarin cim ma sako tsohon karamin minista na ma'aikatar da iyalinsa, wadanda aka yi garkuwa da su a kasar Yemen.

https://p.dw.com/p/Bu2s
Jürgen Chrobg, wanda aka yi garkuwa da shi a kasar Yemen.
Jürgen Chrobg, wanda aka yi garkuwa da shi a kasar Yemen.Hoto: dpa - Bildfunk

Har ila yau dai, tsohon babban jami’in ma’aikatar harkokin wajen Jamus din nan Jürgen Chrobog da iyalinsa na hannun wasu `yan bindigan da suka yi garkuwa da su a kasar Yemen. Ana nan ana ta rade-radi kan ranar da za a sako su. Gwamnatin kasar Yemen din dai ta sha ba da labarai masu jirkitaswa. A wani lokacin ma, sai da aka ce, za a sako su jiya da rana. Amma kuma sai hakan bai wakana ba. Akwai dai alamun da ke nuna cewa, an sami cikas a tattaunawar da ake yi da masu garkuwa da jami’in

Kamar yadda wata jaridar kasar, wato „Yemen Observer“ ta ruwaito, `yan bindigan sun tabbatar mata cewa tattaunawar da ake yi don cim ma sako jami’in ta ci tura. Sai dai, ßangarori da dama na nuna shakku ga wannan labarin, saboda ba a sami tabbacinsa daga ko wace kafa ta hukuma ba. Amma masu sa ido kan batun na hasashen cewa, ci gaba da yin garkuwa da jami’in ma, wata alama ce da ke nuna rashin cim ma daidaito a tattaunawar.

Wasu kafofin da ba a tabbatad da tushensu ba, sun ce ministan harkokin cikin gida na kasar Yemen din da kansa, Raschad al Eleimi da kansa, na cikin masu tattaunawa da `yan bindigan. Jaridar „Yemen Observer“ din dai ta ari bakin daya daga cikin masu garkuwan, yana mai cewar: ba za a cim ma sako jami’in da iyalinsa ba, sai gwamnatin kasar ta amince da duk bukatunsu ba da wani sharadi ba. Ita ko gwamnatin har ila yau, ta ki ta bayyana matsayinta.

Su dai `yan bindigan na neman cim ma sako wasu `yan uwansu guda biyar ne da hukuma ta tsare a gidan yari. Amma sun tabbatar wa jaridar „Yeemen Observer“ cewa, ba za su yi wa jami’in da ke hannunsu wata barazanar halaka shi ba. Kuma sun ce bas a bukatar wani kudi na diyya kafin su sako shi. Burinsu ne kawai, su cim ma sako `yan uwansu da ke tsare a gidan yari.

A halin yanzu dai, ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier, ya dakatad da hutunsa na karshen shekara, ya dawo birnin Berlin, don shi da kansa ya ja akalar hidimomin da ake yi na cim ma sako jami’in. Da yake amsa tambayoyin maneman labarai, bayyana cewa:-

„Abin da zan iya gaya muku a yanzu shi ne, rahotannin da kuke bayarwa a ko wace awa na cewa nan ba da dadewa za a sako jami’in, ba zai taimaka wajen cim ma burinmu ba. Muna bukatar lokaci, da kuma hakuri wajen tinkarar wannan matsalar. Amma na yi imanin cewa, za mu cim ma sakamako kafin karshen wannan shekarar.“

Tun ran larabar da ta wuce ne aka yi garkuwa da tsohon karamin minista a ma’aikatar harkokin wajen Jamus, Jürgen Chrobog da iyalinsa, a gabshin kasar ta Yemen, inda yake kai ziyara ta amsa gayyatar da mukaddashin ministan harkokin wajen kasar ya yi masa. Ban da dai jami’in da iyalinsa, direbobin motarsu, su biyu, da kuma tafinta da jagoransu, dukkansu `yan kasar Yemen din, har ila yau na hannun `yan bindigan.