1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Garkuwa da 'yan ƙetare a yankin Darfur

August 30, 2010

Mayaƙan sa kai a yankin Darfur na Sudan sun yi garkuwa da Rashawa biyu domin neman fansa

https://p.dw.com/p/OzB8
Hoto: picture-alliance/ dpa/dpaweb

Kamfanin dillancin labaran ƙasar Sudan SUNA ya ruwaito sace wasu 'yan Rasha biyu matuƙa jiragen sama a garin Nyala dake yankin Darfur - mai fama da rigingimu a ƙasar Sudan. Sace - sacen 'yan ƙetare domin fansar su da kuɗi ya zama ruwan dare a yankin yammacin Sudan, matsalar da kuma ke janyo cikas ga aikace - aikacen masu bayar da agaji da kuma na dakarun wanzar da zaman lafiyar da Majalisa Ɗinkin Duniya ke ɗaukar nauyin ayyukan su a yankin na Darfur.

Rashawa biyun da aka sacen dai suna yin aiki ne da kamfanin jiragen saman Sudan na Badr Airlines, kana jiya Lahadi ne aka sace su - kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ta Sudan ya faɗi. Galibi matasa daga ƙabilar Larabawa ne dai ke sace - sacen ma'aikatan agaji na ƙetare da kuma dakarun kiyaye zama lafiya a garin na Nyala, wanda shi ne mafi girma a yankin Darfur, inda suke neman kuɗi gabannin sakin su. Wata ma'aikaciyar ƙungiyar bayar da agaji ta Amirka mai suna U.S Charity Samaritan's Purse ta shafe fiye da kwanaki 100 ana garkuwa da ita.

Aikin yin garkuwa da 'yan ƙetare domin neman fansa ya yi ƙamari ne tun bayan da kotun duniya dake shari'ar manyan laifuka ta bayar da sammacin cafke shugaba Umar al-Bashir na ƙasar Sudan bisa zargin aikata laifukan yaƙi a yankin na Darfur.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Abdullahi Tanko Bala