1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta sami nasarar kaiwa ga zagayen kusa dana ƙarshe

Tanko Bala, AbdullahiJune 20, 2008

Jamus ta doke Portugal da ci uku da biyu a gasar cin kofin Nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/ENJt
Kaptin ɗin Jamus Michael Ballack, a dama tare da Christoph Metzelder ke murna bayan nasarar Jamus akan Portugal.Hoto: AP

A cigaba da gasar cin kofin ƙwallon ƙafa na Nahiyar Turia, Jamus ta doke takwararta ta Portugal da ci uku da biyu domin kaiwa ga zagaye na gaba, na kusa dana ƙarshe.


A yanzu dai Jamus ta nuna cewa da gaske take, ta kuma zage dantse domin sake ɗaukar kofin zakaran ƙwallon ƙafa na Nahiyar Turai a karo na huɗu bayan da ta doke Portugal da ci uku da biyu a gasar wasannin da suka buga a ranar Alhamis.

Ɗan wasan Jamus Bastian Schweinsteiger ya sami sanya ƙwallo ta farko a ragar Portugal a zagayen farko a daidai miniti ashirin da biyu da fara wasa.


Ƙungiyar ta Jamus ta kuma nuna cewa ba kanwar lasa bace inda bayan miniti huɗu kacal ta kuma zura ƙwallo ci na biyu a ragar Portugal. Miroslav Klose ya sanya ƙwallon a raga cikin nutsuwa ba da tashin hankali ba.


Nuno Gomes ɗan wasan Portugal ya farkewa ƙungiyarsa ci guda inda shima ya sami jefa ƙwallo a ragar Jamus, sun kuma sami ci na biyu ta hannun Cristiano Ronaldo.


To amma Kaptin ɗin Jamus Michael Ballack wanda ya ƙware kan abin da ya saba, yayin da Schweinsteiger ya turo masa ƙwallo ba tare da ɓata lokaci ba, sai ya doka ta da ka zuwa ragar Portugal. Hakan dai ya baiwa Jamus nasara da ci uku da biyu.


Ko da yake alámura sun so su sha banban inda a miniti na 87 ɗan wasan Portugal Helder Postiga ya kusa jefa ƙwallo a ragar Jamus, to amma masu tsaron gida na ƙungiyar Jamus Arne Frieddrich da Philipp Lahm suka hana shi sakat kamar yadda basu ƙyale Ronaldo yayi tasiri ba.


Wannan dai ya kasance wasa mai armashi da matuƙar muhimmanci ga Jamus duk da dakatarwar da hukumar wasan ƙwallon kafa ta UEFA ta yiwa mai horar da yan wasan na Jamus Joachim Loew.


Bastian Schweinsteiger ya baiyana wasan da cewa babbar nasara ce a gare su. "Yace na yi farin ciki mun yi nasara, a yanzu muna daga cikin ƙungiyoyi huɗu dake kan gaba. A gani na muna da´yan wasa masu kyau kuma mun nuna cewa za mu iya".


Shi ma a nasa bangaren Lukas Podolski yayi bayani inda yace " Ina tsammanin wannan wasa ne sosai na gani na faɗa domin ƙungiyar mu ta nuna bajinta kuma haka ya kamata mu cigaba da yi, kada mu sake mu yi kuskure ko mu saki jiki cewa mune zakarun nahiyar Turai".


A yanzu dai Jamus zata kara a gasa ta gaba da ƙungiyar da ta yi nasara a tsakanin Croatia da Turkiya.