1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

080808 Olympia Eröffnung

Gui, Hao (DW Chinesisch) August 8, 2008

An ƙaddamar da shagulgullan buɗa gasar Olympic ta duniya a birnin Pekin

https://p.dw.com/p/Et8m
Bikin buɗa gasar Olympic ta duniyaHoto: AP




A birnin Pekin na ƙasar China, an ƙaddamar da bikin gasar Olympic ta duniya karo na 29.

kaɗan kenan daga kaɗe kaɗe da waƙe waƙe da aka rera albarkacin buɗe gasar ta Olympic karo na 29  a birnin Pekin.

Bayan lokaci mai tsawo ana kai ruwa rana, a ƙarshe dai a ƙalla mutane dubu 91, wanda suka haɗa da shugabani ƙasashe da dama suka halarci bikin buɗe wasannin a babban filin wasa na birnin Pekin.

Daga sahun shugabanin da suka halarci wannan biki, akwai Georges na Amurika da Nikolas Sarkozy, shugaban Ƙungiyar Tarayya Turai kuma shugaban ƙasar France.

Jim kaɗan kamin fara bikin shugaban gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta aika sako, inda ta yi fatan ya wakana lami lafiya.

Gasar ta wannan karo da ake kyauttata zaton ta fi sauran tasiri, ta samu halartar tawagogi 204 daga sassa dabam dabam na duniya.

A jawabin da ya gabatar shugaban komitin Olympic na duniya Jacques Rogges, yayi yabo da jinjina dantse da komitin daya shirya wannan gasa ,tare kuma da yabawa birnin Pekin a game da matakan da ya ɗauka don cimma nasara.

Bayan jawani Jacque Rogges shugaban ƙasar China Hu Jintao ya buɗa gasar a hukunce:

" Lalle maraba da baƙi,birnin Pekin na maku sanu da zuwa, da fatan za a yi shagulgulla lami lafiya".

Bayan jawabin shugaban ƙasa,wani ɗan wasan motsa jiki ne na ƙasar China Li Ning ya kunna fitilar Oplympic bayan ta kewaya duniya  a tsawan kilomita dubu 137, tun daga ranar 24 ga watan Maris.

Zagayen da fitilar tayi, ya hadasa cece- kuce nan da cen.

Jim kaɗan kafin buɗe wassan, jami´an tsaro, sun bayyana wata barazanar kai hari a kan wani jirgi mallakar kamfanin jiragen sama na China Air, to saidai bayan bincike, sun gano cewar babu wata matsala.

ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bani adama, sun yi amfani da wannan dama, domin faɗakar da jama´a  a game da halin da ake ciki ,ta fannin kare haƙƙoƙin bani adama a ƙasar China.

Ƙungiyar ´yan jarida ta ƙasa da ƙasa wato,"Reporters sans Frontiéres" ta girka wata tashar FM sukutum a birnin Pekin, inda zata watsa shirye shirye, da suka jiɓancin ´yancin ɗan adam, a duk tsawan lokacin gasar Olympic ta duniya.