1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gasar wasan dambe

Mouhamadou Awal Balarabe
May 2, 2017

Shahararren dan damben nan na Ingila Anthony Joshua ya yi wa Vladimir Klitscko da ke rike da bajintar duniya fintinkau a karawar da suka yi a Wembley.

https://p.dw.com/p/2cF4s
Wembley Boxen  Wladimir Klitschko vs Anthony Joshua
Hoto: Reuters/A. Couldridge

Wannan gagarumin ƙwazo ya sa Joshua mai shekaru 27 da haihuwa ci gaba da rike kambunsa ta IBF. Sannan kuma ya kwace lambar zakaran boksin ajin masu nauyi ta duniya daga hannun Wladimir Klitschko mai shekaru 41 a filin wasa na Wembley.

'Yan kallo kimanin dubu 90 ne suka shaida karawar da aka shafe zagaye 11 ana yinta kafin Anthony Joshua ya kai abokin karawarsa kasa bayan wani wawan naushi da ya sa alkali tsayar da wasa.

Shi dai Anthony Joshua, wanda iyayensa 'yan Najeriya ne, ya taba lashe lambar zinariya ta dubiya a wasannin Olympik na 2001. Sannan kuma wannan shi ne karo na 19 da ya nuna bajintar lashe damben da fintikau.