1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gauck: Zan sauka daga mulkin Jamus a 2017

Abdul Raheem Hassam/ MABJune 6, 2016

Shugaban tarayyar Jamus Joachim Gauck ya ce ba zai nemi sabon wa'adin mulki ba a shekara mai zuwa saboda ya fara tsufa.

https://p.dw.com/p/1J1Kk
Deutschland Joachim Gauck
Hoto: Reuters/H. Hanschke

Shugaban kasar Jamus Joachim Gauck ya bayyana aniyarsa na sauka daga karagar mulki idan wa'adinsa na farko ya kare a shekara mai zuwa. Shi shugaban mai shekaru 76 a duniya, ya nunar a birnin Berlin cewa, ba shi da karfin gudanar da wani sabon wa'adin mulki yadda ya kamata anan gaba.

Ya ce "Ina farin cikin kasancetw cikin koshin lafiya. Amma kuma ina sane da cewa rayuwa za ta banbanta tsakanin yanzu da lokacin da zan tinkari shekaru 77 zuwa 82 a duniya. Ba ni da tabbacin samun kuzarin gudanar da wa'adin mulki na shekaru biyar nan gaba."

Ko da shi ke shugaban kasa mukami ne na jeka-na-yika a Jamus, amma tuni aka fara hasashen manyan jami'an gwamnatin da za a iya tsayarwa takara, daga cikinsu kuwa har da ministan Kudi Wolfgang Schäuble da ministan harkoki wajen kasar Frank-Walter Steinmeier.