1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Gobara ta hallaka mutane da dama

Gazali Abdou Tasawa
October 8, 2017

Mahukuntan kasar Ghana sun tabbatar da mutuwar mutane shida a sakamakon wata gobara da ta tashi a daren Asabar daga wata tankar dakon gas ta kuma yadu zuwa wasu gidajen mai na birnin Accra.

https://p.dw.com/p/2lSwM
Ghana Explosion in Tankstelle
Hoto: Reuters/@ronnieamofa

Mahukuntan kasar Ghana sun tabbatar da mutuwar mutane shida a yayin da wasu 35 suka ji rauni a sakamakon wata gobara da ta tashi a cikin daren jiya Asabar daga wata tankar dakon gas ta kuma yadu zuwa wasu gidajen mai guda biyu a birnin Accra da ke kusa da inda aka ajiye motar. 

Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa gobarar ta yi wa gidajen man kaca-kaca tare da haifar da rudani a tsakanin mazauna unguwar da suka yi ta barin gidajensu a guje musamman a sakamakon irin karan da ya ta tashi a lokacin gobarar. 

Shugaban kasar ta Ghana Nana Akufo Addo ya isar da ta'aziyyarsa ga al'ummar kasar a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya yi alkawarin daukar matakan da suka dace domin ganin irin wannan hadari bai sake abkuwa ba. 

A wannan Lahadi kuma mataimakin shugaban kasar ta Ghana Mahamadu Bawumia ya kai ziyara a inda hadarin ya auku.

Mutane 150 suka halaka a cikin wata gobarar mai kama da wannan da ta wakana a shekara ta 2015 a wani gidan mai na birnin Accra.