1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana na samun bunƙasar tattalin arziƙi

June 25, 2010

A daura da kyakkyawan ci gaba a ƙwallon ƙafa ƙasar Ghana kazalika tana samun bunƙasar tattalin arziƙi akwai kuma fatan cewar al'umar ƙasar zasu ci gajiyar man fetir da aka gano a cikinta baya-bayan nan

https://p.dw.com/p/O3Gt
Al'umar Ghana na fatan cin moriyar arziƙin man fetur da Allah Ya fuwace wa ƙasarsuHoto: Stefanie Duckstein

Da farko dai zamu fara ne da sharhin jaridar Die Tageszeitung, wadda a wannan makon ta leƙa ƙasar Libiya domin duba halin da 'yan gudun hijira ke ciki a gidajen kurkuku da mahukuntan Libiya ke tsare da su suna kuma nuna musu azaba da sauran matakai na rashin imani. Jaridar ta ce:

UN USA Libyen Muammar al Gaddafi bei der Volversammlung in New York
Ana sukan lamirin shugaba Ghaddafi dangane da muzanta wa fursinoni da mahukuntansa ke yiHoto: AP / United Nations

"Duk wanda tsautsayi ya rutsa da shi ya faɗa sansanin gwalegwale na Garabule dake ƙasar Libiya tilas ya fid da duk wata ƙauna game da makomar rayuwarsa. Akan cusa fursinoni arba'in zuwa hamsin ne a cikin ɗakin kurkuku guda mai makewayi guda ɗaya ƙwal. Da wuya fursinonin kan samu ruwan sha sai dai jefi-jefi kuma sau ɗaya ake ƙyale su su fita farfajiyar gidan fursunan a mako. Wasu daga cikin fursinonin ma dai sun yi wata-da-watanni ana tsare da su a sansanin gwalegwalen ba tare da an nuna musu ainihin lafin da suka aikata ba. Sansanin na Garabule dake da tazarar kilomita 40 daga fadar mulki ta Tripoli yana ɗaya ne daga cikin sansanonin gwalegwale na Libiya inda ake tsare fursinoni, galibi 'yan gudun hijira daga Afirka, ba ma tare da kula da lafiyarsu ba."

A daura da ƙwallon ƙafa ƙasar Ghana na samun ci gaban tattalin arziƙi duk da matsaloli na kuɗi da tattalin arziƙin dake addabar duniya. Jaridar Neues Deutschland tayi amfani da wannan dama domin duba tarihin dangantakar tattalin arziƙi tsakanin Ghana da Jamus inda ta ce:

"Ƙasar Ghana tana ci gaba da nuna kuzari a al'amuran tattalin arziƙinta inda a shekarar da ta wuce ta samu bunƙasar kashi 5.9 cikin ɗari. Ƙasar dai duk da ɗimbin basusukan ƙetare dake kanta tana ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka na kudu da hamadar Sahara dake samun nasarori ga tattalin arziƙinsu. Kamar dai a zamanin baya har a yau ma akwai ƙaƙƙarfar dangantakar tattalin arziƙi tsakaninta da Jamus, inda a baya ga ƙwayar koko, Jamus ke cinikin katako da sauran ma'adinai masu muhimmanci ga masana'antunta. Gaba ɗaya dai Ghana ce a rukuni na 93 tsakanin ƙasashen da Jamus ke hulɗa da su a cinikinta na ƙetare."

Ita ma dai jaridar Berliner Zeitung ta ba da la'akari da bunƙasar tattalin arziƙin Ghana, musamman ma sakamakon ɗimbim adanin man fetur da aka gano a ƙasar, wanda ake fama zai amfanar da al'umarta. Jaridar ta ce babban abin da al'umar Ghana ke fata shi ne gwamnati tayi amfani da dubban miliyoyin na ribar da zata samu daga cinikin mai wajen kyautata makomar jin daɗinsu da kuma inganta hanyoyin sadarwa, musamman na mota, waɗanda a halin yanzu suka taɓarɓare sakamakon ruwan sama da ake yi kamar da bakin ƙwarya a ƙasar a baya-bayan nan."

A sakamakon rashin damina mai albarka a yankin sahel da ya haɗa da Niger da Chadi da Mali da kuma Mauritaniya, ana buƙatar taimakon abinci don kauce wa barazanar yunwa, kamar yadda jaridar Die Tageszeitung ta rawaito ta kuma ƙara da cewar:

"Ana buƙatar aƙalla taimako na jumullar kuɗi dalar Amirka miliyan 205 don tallafa wa mabuƙata, amma kawo yanzu kashi 50% na waɗannan kuɗaɗe aka samu. An fuskanci irin wannan matsalar a misalin shekaru biyar da suka wuce a ƙasar Nijer, inda lamarin yayi tsamari sakamakon sako-sako da kafofin ba da taimako suka yi da matsalar."

Mwallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu