1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Zabe ya gudana lafiya

Ahmed Salisu
December 1, 2016

Al'ummar kasar Ghana sun kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa lami lafiya ba tare da fuskantar wani tashin hankali ba.

https://p.dw.com/p/2Taeu
Ghana Wahlen Abstimmung Auszaehlung Warten
Shirin kada kuri'a a zaben shugaban kasa a GhanaHoto: AP

Al'ummar kasar Ghana sun gudanar da zaben shugaban kasa ranar bakwai ga watan Disambar nan na shekarar 2016 ba tare da fuskantar wani kalubale babba ba. Takara dai ta fi zafi ne tsakanin shugaban kasar mai ci yanzu John Dramani Mahama da kuma Nana Akufo-Addo sai kuma wasu 'yan takara abiyar da suka hadar da dan takarar Independa.