1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gidauniyar Kofi Annan

September 17, 2007
https://p.dw.com/p/BuB5

Dayake bayyana miliyoyin mutanen da suka jikkata daga ambaliyan ruwa a nahiyar Afrika,Tsohon jagoran mdd Kofi Annan yayi gargadin cewa ,sauyin yanayi zai kasance babban kalubale wa biladama anan gaba.

Mr Annan yace zai sanya fifiuko kann kwararan yan gudun hijira da matsaloli da biladama zasu fuskanta,sakamakon sauyin yanayi ,a sabon shirinsa dazai kaddamar ranar 17 ga watan okoba mai kamawa.

Ya fadawa taron manema labaru a birnin GEneva cewar,sauyin yanayi ya fara addabar daruruwan alummomin duniya,batu dake zama babban kalubale ga biladaman.

Wannan sabon shirin tallafi da tsohon sakataren mdd da hadin gwiwar gwamnatin Swizaland ke daukar nauyin kaddamarwa,nada nufin rufe gibin a rarraba kayyayakin agaji,kare gibin,ta hanyar harhada kawunan gwamnatoci da kungiyoyin bada agaji da sojoji da yan kasuwa,da kwararrun masana.