1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

270910 Israel Baustopp Friedensgespräche

September 27, 2010

Ana Fargaban kan makomar tattaunawar samar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya, bayan da aka koma gina matsugunan yahudawa.

https://p.dw.com/p/PNlk
Sabbin matsugunan YahudawaHoto: picture-alliance/dpa

Makwanni huɗu bayan komawa ga tattaunawar da aka dakatar shekaru biyu, don samar da zaman lafiya tsakanin Yahudawa da Palasɗinawa, yanzu wani cikas ya kunno kai, bayan da a daren jiya, Isra'ila ta ɗage dokar dakatar da gina matsugunan Yahudawa. Dama dai Palasɗinawa sun gitta sharaɗin cewa, idan a ka koma ga gina matsugunan Yahudawa to su kuwa za su fice daga tattaunawar da bata kai ko'ina ba.

Su dai Yahudawa 'yan kaka gida sun yi shagalin nuna murna ga kawo ƙarshen dakatar da gine-gine da aka yi a yankin falasɗinawa da ke yammacin Kogin Jordan. A yayin wannan shagalin, wani mawaƙi bayahude ya kira shugaban Amirka da sunansa na musulunci ya ce "Husaini Obama ka sani cewa Isra'ila ƙasa ce ta Isra'ilawa". Shi kuwa ministan sufuri a jawabinsa na kawo ƙarshen wa'adin dakatar da ginin yace:

"Daga tsakiyar daren litinin, duk waɗanda ke da izinin gini to su ci gaba da gina gidajensu. Ina so na godewa Firai minista Netanyahu jagoran jam'iyar Likud, wanda ya bada himma kan hakan, kuma yake jagorantar samar da zaman lafiya"

Nahost Israel Palästinenser Siedler Baustopp beendet
Motoci dake a wurin matsugunan YahudawaHoto: AP

Ko da a shekaran jiya ma dai, Firai ministan na Isra'ila ya buga waya wa sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton, da shugaban ƙasar Masar Hosni Mubarack da kuma Sarki Abdallah na Jodan, duk gabanin yanke shawarar sake gine-ginen. Dama dai shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas ya lashi takobin cewa muddin a ka koma ga gina matsugunnan Yahudawa 'yan kaka gida, to shi kuwa zai fice daga tattaunawa.

Shugaba Abbas ya bugawa Natenyahu waya, inda ya ce masa abune mai kyau a ci gaba da tattaunawa domin kafa tarihi. Duk da rahotonnin da kafafen yaɗa labaran Isra'ila ke ta watsawa na cewa, duk da ci gaba da gine-ginen za'a ci gaba da tattaunawa, amma akwai waɗanda ke shakkan hakan.

Shi kuwa Tzachi Hanegbi dake ɗan majalisar dokokin Isra'ila daga jam'iyar adawa ta Kadima, ya ce shi ma kansa shugaban Amirka, ya yi suɓarda baka a jawabin da ya yi gaban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya.

"Shugaban ƙasar Amirka, a jawabinsa gaban tsauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce buƙatun Palasɗinawa sun yi yawa, don haka da wuya a iya rage su. Wannan shine dalilin da ya sa ba a samu cimma wani abu ba, ko da yake mun son buƙatar mu ita ce ake son cimma a nan da watani masu zuwa"

Shi dai shugaba Obama ya faɗawa taron cewa nan da shekara guda Palasɗinawa na iya samun wakilci a Majalisar Ɗinkin Duniya, amma dai za a ci gaba da gina matsugunan Yahudawa 2000, waɗanda gwamnatin Isra'ila ta bada izinin ginawa.

Shi kuwa Tamar Shapira wani bayahude ne ɗan fafitaka dake cikin tawagar yahudawa dake Allah wadai da yadda Isra'ila ke muzgunawa Palasɗinawa kuma yanzu suna kan hanyarsu ta kai agaji izuwa Gaza, domin karya datsewar da Isra'ila ta ke yi wa yankin.

Waffenruhe Israel Gaza Panzer im südlichen Israel
Sojojin Isra'ila a iyakarsu da GazaHoto: AP

"A ko da yaushe, Isra'ila, ta saba yin parfaganda, wai tsaron kanta ta ke yi, Isra'ila takan nuna cewa ita ma, tana fiskantar matsala, wannan haka aka ko ya min tun ina yaro, da haka na girma, har na shiga soja, wai domin na zama sojan da zai kare kansa".

Wannan dai wani ƙalubale ne ga Isra'ila, domin ƙungiyoyin fafitaka na ci gaba da yunƙurin karya datsewar da ta ke yi wa Gaza, ga kuma yanzu batun ci gaba da gina matsugunan yahudawa wanda ƙasa da ƙasa ke adawa da shi.

Mawallafa: Usman Shehu Usman da Sebastian Engelbrecht

Edita: Yahouza Sadissou Madobi