1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

girgiza ƙasa a Zimbabwe da Mozambique

February 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bv71

Tun da sanhin sahiyar yau,wata girgiza kasa,mai karfin 7 da dugu 5 a ma´aunin Richter, ta wakana, a ƙasar Zimbabwe da arewancin Mozambique.

A Zimbabwe, ƙarfin girgizar da ya kai har garin Bulawayo dake tazara kilomita 450 a kudu maso gabancin Arare, babban birnin ƙasar, ya sa mutane shiga halin rudani.

Kafofin sadarwa na ƙasashen 2, sun yi kira ga jama´a da ta kwantar da hankulla.

A hali yanzu, rahotani sun ce, mutane 2 ne,su ka rasa rayuka a sanadiyar wannan girgiza ƙasa.