1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girgizar kasa a nahiyar Asia.

December 26, 2004

Irin barnar da girgizar kasar ta Haifar a kasar Srilanka

https://p.dw.com/p/Bve1
Hoto: AP

Kamar yadda kukaji a labaran duniya wan nan girgizar kasa da aka fuskanta a tsibirin Sumatra na kasar indonesia a yanzu haka naa matsayin irin ta da ba a taba fuskanta ba a doron kasa kusan tsawon shekaru 40 da suka gabata.

Hakan kuwa ya faru ne a sabili da irin barnar da wan nan girgizar kasa tayi ba ma a kasar ta Indonesia ba kawai har ya zuwa kasashen kudu maso gabashin Nahiyar asia da suka hadar da Srilanka da India da Malaysia da Thailand Da kuma Myanmar.

Rahotanni dai daga wan nan yanki na Sumatra ya nunar da cewa wan nan girgizar kasa ta afku ne a tsakiyar Teku dake kusa da wan nan tsibiri,wanda hakan ya haifar da wata igiyar ruwa mai karfin gaske da ake kiran ta da suna Tsunamis,inda karfin ta ya haifar ta nausa izuwa kasashen dake kudu maso gabashin yankin na Asiain,wanda hakan shine ya bata damar yin ta,adi na rayuka da kuma dukiyoyin mutanen wadan nan kasashe na sama da muka Ambata.

A cewar masu nazarin yanayin kasa, wan nan girgizar kasa ta kai tsawon mita takwas da digo tara a ma,aunin Richter,wanda keda munin gaske a tarihin girgizar kasa a duniya baki daya.

Ya zuwa yanzu Rahotannin da suka iske mu wan nan girgizar kasa tayi sanadiyyar mutuwar Mutane sama da dubu 2 da dari 500 a can kasar srilanka banda wasu da daman gaske kuma da suka bace.

Daga can kuwa kuwa kasar India bayanai sun shaidar da cewa mutane dubu 2,437 suka rugamu gidan gaskiya ban da mkuma wasu daruruwa da suka bace sama ko bisa sakamakon faruwar wan nan Al,amari.

Kasar indonesia, inda wan nan girgizar kasa ta faru a cikin wani tsibiri dake yankin ta, mutane a kalla dubu 1,873 suka rasa rayukan su banda wasu mutane masu yawahn gaske da aka neme su sama ko bisa.

Bugu da kari wan nan girgizar kasa ta kuma haifar da mutuwar mutane a kalla 279 a can kasar Thailand ta hanyar igiyar ruwan nan da aka fi sani da suna tsunamis,banda wasu kuma dubu biyar da suka bace.

Kasar Malaysia ma wan nan al,amari ya shafe ta,a inda Rahotanni suka bayar da sanarwar mutuwar mutane 28 a hannu daya kuma da bacewar wasu mutanen guda dari.

A karshe kasar Mayanmar da akafi sani da suna Burma, ita tzayi asarar mutane a kalla goma ta hanyar ambaliyar igiyar ruwan nan ta Tsunamis.

A gabaki daya a cewar kamfanin dillancin labaru na reuters mutane a kalla dubu bakwai ne suka rasa rayukan su a cikin wadan nan kasashe shida da muka ambata,wasu kuma miliyan daya suka rasa gidajen kwanan su banda kuma barnar dukiyoyi na miliyoyin daloli da girgizar kasar ta haifar.

Bugu da kari bayanan sun kuma shaidar da cewa rashin kyakyawan hanyoyin sadarwa na kawo cikas na kalailaice irin barnar da wan nan girgizar kasa tayi kama dai daga rayukan mutane da kuma dukiyoyin su.

A waje daya kuma akwai bayanai dake nuni da cewa wan nan igiyar ruwa mai karfin gaske ka iya shafar wasu kasashe na gabashin nahiyar Africa ta tsibirin nan na Comoros,to sai dai kuma babu tabbas game da hakan.

Ya zuwa yanzu dai kasashen da wan nan abu ya shafa tuni sukayi kira ga kasashen duniya masu hannu da shuni dasu kawo musu dauki na tallafi don ceton rayukan iyalan wadan da wan nan abu ya rutsa dasu.

Tuni dai kungiyyar bayar da agajin gaggawa ta Red Cross ta aike da tawagar jamian ta izuwa wadan nan kasashen don bayar da aikin agaji na kayayyaki da aka kiyasta kudin su izuwa yuro miliyan dari biyar.

Game kuwa da wan nan kira da kasashen sukayi tuni kungiyyar gamayyar turai tayi alkawarin tallafi na yuro miliyan uku ga wadan nan kasashe don agazawa iyalan wadan da wan nan abu ya shafa.

Ya zuwa kuwa lokacin da muke baku wan nan rahoto babu wani cikakken labari dake nuni game da karfaffen dalilin daya haifar da faruwar wan nan girgizar kasa dake irin ta ta farko a doron kasa a shekaru arbain da suke gabata.

Ibrahim Sani.