1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girgizar Kasa Ta Tsunami A Asiya

December 30, 2004

Fargar jaji da kwararru ke yi bayan tsautsayin da ya rutsa da yankin kudancin Asiya ba zai tsinana kome wajen sassauta radadin dake tattare da jama'a a wuraren da bala'in ya shafa ba

https://p.dw.com/p/Bvdv

Kamar dai yadda aka saba gani a ko da yaushe aka fuskanci wani bala’i daga Indallahi, a wannan karon ma kwararru sun shiga tofa albarkacin bakinsu a game da matakan da za a iya dauka domin riga kafin mutuwar dubban mutanen da bala’in ambaliyar ruwan da girgizar kasa ta haddasa a kudancin Asiya ya rutsa da su. An samu masu batu a game da wata fasaha ta gangami akan lokaci, wai kamar yadda yake a yankin tekun Pacific, ko kuma wani dan kasar Australiya dake ikirarin cewar wai ya gabatar da gargadi amma sai aka yi ko oho da shi. Ire-iren wannan fargar jajin ba ya da amfani kuma ba zai tsinana kome ba wajen sassauta radadin da dubban daruruwa ko kuma ma miliyoyin mutane ke ciki, wadanda suka yi asarar dangi da kadarorinsu a yankunan da bala’in ya shafa. Kai hatta mahawara akan batun bata da alfanu. Mu dauka ma cewar akwai irin wannan fasaha ta gangami, to shin mutane zasu samu isasshen lokaci domin hayewa tudun natsira. Kuma ma ta yaya wannan gangamin zai isa ga mutanen da lamarin ya shafa. Babu dai wani daya daga cikin kwararrun dake tofa albarkacin bakinsu da ya fito fili ya amsa wadannan tambayoyi. Ire-iren girgizar kasar da aka sha fuskanta a sauran sassa na duniya sun yi daura da ikirarin da kwararrun suke yi. Misali dai garin Bam mai dadadden tarihi a kasar Iran, ya fuskanci girgizar kasa a daidai irin wannan lokaci, shekarar da ta wuce. Kuma wannan ba shi ne karo na farko ba. Amma fa har yau ba wanda yayi kurarin canza wa garin mazauni. Yana nan ne daidai wurin da da zarar wata sabuwar girgizar ta taso zata yi kaca-kaca da shi. Wannan maganar daidai take akan yankunan dake gabacin birnin Istanbul na kasar Turkiyya, wadanda ke shan fama da girgizar kasa. Akan sake gina wadannan yankuna kuma mutane su sake komawa gidajensu kamar dai ba wani abin da ya faru, suna masu jiran sabuwar girgizar kasar da zata taso, wacce kuma ba makawa game da ita. A hakikanin gaskiya babu wani abin da dan-Adam ke da ikon tabukawa domin hana wanzuwar bala'i daga Indallahi. Duka-duka abin da zai iya yi shi ne koyan darasi da kuma neman hanyoyin sassauta wannan barazana ga makomar rayuwarsa. Misali wajen canza mazauninsa zuwa yankuna marasa hadari. Amma a saboda wasu dalilai, ko dai na tattalin arziki da zamantakewa ko kuma sabo, dan-Adam sai ya gwammance yayi ko in-kula da lamarin ya ci gaba da rayuwarsa a wadannan wurare duk da sikankancewarsa da hadarin dake tattare da shi dangane da makomar rayuwar tasa. Mantuwa dai dabi’a ce ta dan-Adam kuma watakila wannan shi ne muhimmin makamin da Allah Ya fuwace masa domin ci gaba da rayuwa a doron kasa.